Kai tsaye: Yadda zagaye na 2 na zaben gwamnan Osun ke ta gudana

Kai tsaye: Yadda zagaye na 2 na zaben gwamnan Osun ke ta gudana

- Zagaye na biyu na zaben gwamnan Osun na cigaba da gudana

- Ana gudanar da zaben a mazabu 7

Yanzu yanzu labarin da muke samu da majiyoyin na nuni ne da cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC ta soma gudanar da zagaye na biyu na zaben gwamnan jihar Osun kamar dai yadda ta tsara a karshen makon da ya gabata.

Kai tsaye: Yadda zagaye na 2 na zaben gwamnan Osun ke ta gudana

Kai tsaye: Yadda zagaye na 2 na zaben gwamnan Osun ke ta gudana
Source: Original

Inda mai karatu bai manta ba hukumar ta INEC ta bayyana sakamakon karshe na zaben gwamnan jihar Osun inda tace bai kammalu ba sai an je zagaye na biyu.

KU KARANTA: Ambaliyan ruwa yaci hanyar kauyen su Jonathan

Legit.ng ta samu cewa hukumar zaben ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba saboda cewa kuri'un da aka soke a zaben sun fi kuri'un tazarar dake tsakanin manyan 'yan takarar na jam'iyyar PDP da kuma APC.

Sakamakon zaben dai kamar yadda muka samu ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar adawa a jihar na PDP mai suna Sanata Ademola Adeleke 254,698 yana da kuri'u yayin da shi kuma dan takarar jam'iyya ma mulki na APC mai suna Gboyega Oyetola yana da kuri'u 254,345.

Ga dai jadawalin inda za'a sake yin zaben a zagaye na biyu:

Ife North - Ward 10, PU2

Ife South - Olode Ward 07, PU12, Adereti Village

Ife South - Osi Ward 8 PU10, Aluti Erin Primary School, Albert village

Orolu - Ward 08 PU001, Kajola village

Orolu - Ward 08 PU004 Idi Iya village

Orolu - Ward 09 PU 003 Gbogbo Primary School Adeleke

Osogbo - Ataoja Ward 05 PU 017 Adewale

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel