Yanzu lokaci ne da Matasa irin mu za su mulki kasar nan – inji Bukola Saraki

Yanzu lokaci ne da Matasa irin mu za su mulki kasar nan – inji Bukola Saraki

Yayin da ake cigaba da buga tamburan 2019, labari ya zo mana cewa jirgin yakin daya daga cikin masu neman kujaran Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP ya shiga Mahaifar Shugaban kasa Buhari.

Yanzu lokaci ne da Matasa irin mu za su mulki kasar nan – inji Bukola Saraki

PDP tace za tayi nasara a Jihar Katsina da kuma zaben Shugaban kasa
Source: Twitter

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki wanda yana cikin masu neman takara a PDP ya shiga Jihar Katsina Ranar Laraba inda yake neman goyon bayan ‘Ya ‘yan PDP wajen zaben fitar da gwani da za ayi kwanan nan.

Bukola Saraki ya fadawa manyan PDP a Jihar ta Katsina cewa lokaci yayi da za a zabi Shugaba na gari kuma Matashi. Saraki yace ya kamata Matasa irin sa su ja ragamar kasar nan domin kuwa yanzu haka ake yi a fadin Duniya.

KU KARANTA: Dankwambo yayi alkawarin maida Boko kyauta idan ya samu mulki

Tsohon Gwamnan ya bayyana cewa Katsinawa mutanen sa ne inda yace yayi aiki tare da Marigayi Ummaru Musa ‘Yaradua sannan kuma tsohon Gwamna Ibrahim Shema aminin sa ne. Saraki yana sa sa rai PDP ta ba sa tuta a 2019.

Shugaban PDP na Jihar Salisu Majigiri ya bayyana cewa PDP ta kara karfi tun bayan da Shugaban Majalisar Kasar Saraki ya dawo Jam’iyyar bayan ya fice daga APC. Majigiri yace PDP za ta yi nasara a zabukan da za ayi a badi.

A baya kun ji cewa PDP za ta tsaida Sanata Lado Danmarke ne a matsayin ‘Dan takarar Gwamna a Jihar ta Katsina a zabe mai zuwa domin ya kara da Gwamna Aminu Masari na Jam’iyyar APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel