Yaki da rashawa: Magu ya yiwa 'barayin gwamnati' sabuwar albishir

Yaki da rashawa: Magu ya yiwa 'barayin gwamnati' sabuwar albishir

- Shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya gargadi wadanda suka sace dukiyar kasa su garzaya dawo da su ko su fuskanci fushin hukuma

- Magu ya ce akwai alamar cin nasara kan yaki da rashawa a Afirka idan akwai hadin kai tsakanin hukumomin tsaro da hukumomin yaki da rasahwa

- Shugaban na EFCC, ya ce an samu ragowar ayyukan laifi a Najeriya saboda hukumomin tsaro ba su ragawa mas aikata laifi

Ibrahim Magu, Shugaban riko na hukumar yaki da rashawa na Najeriya EFCC ya gargadi dukkan wadanda suka sace kudaden al'umma da ga asusun gwamnati su garzaya dawo da su idan kma ba haka ba za su fuskanci hukunci.

A hirar da Magu ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a birnin New York da Amurka, ya ce rashawa abu ne mai illa wadda ba za'a amince ta cigaba da yaduwa a Najeriya ba.

Yaki da rashawa: Magu ya yiwa 'barayin gwamnati' sabuwar albishir

Yaki da rashawa: Magu ya yiwa 'barayin gwamnati' sabuwar albishir
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kwartanci: An anjiye ma'aikacin gwamnatin jihar Katsina a gidan kaso

Legit.ng ta gano cewa Magu ya ce: "Ya kamata dukkan wadanda suka diba kudaden gwamnati su dawo da su, su taimaka mana wajen yakar rashawa saboda muhimmancin da ta ke da shi."

"Nauyin yaki da rashawa ya rataya a kawunnan dukkan mu, Da wadanda su kayi satar da wanda ba suyi ba. Abinda na ke ganin ya da ce shine duk wanda suka saci kudin su dawo da su, sai mu ga abinda za mu iya yi akansu."

Magu kuma ya ce idan kuma ba su amsa kirar hukumar sun dawo da kudaden ba, tabbas doka za ta damko su komin dadewa.

Ya kuma ce akwai alamun cewa Afirka za tayi nasara kan yaki da rashawa idan akwai hadin kai tsakanin hukumomin tsaro da hukumomin da ke yaki da rashawa. Ya kara da cewa EFCC tana hadin gwiwa da takwarorinta na kasashen Afirka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel