Direban Aso Villa ya yi yunkurin kashe kansa saboda karancin albashi

Direban Aso Villa ya yi yunkurin kashe kansa saboda karancin albashi

An ceto wani tsohon direban fadar shugaban kasa dake Villa, Sunday Offre daga kan bishiyar da ya rataye kansa a lokacin da yayi yunkurin kashe kansa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Offer wanda ya fito daga jihar Cross River yana kan mataki na uku ne inda ake biyansa albashi N25,000 a duk wata.

An tattaro cewa tun a shekarar 2009 ne ya fara aiki a fadar shugaban kasar.

Ma’aikatan fadar shugaban kasar sun bayyana cewa an gano direban mai ýaýa biyu a wani daji a Kubwa, wani yanki na babban birnin tarayya Abuja inda yake yawo a saman bishiya.

Direban Aso Villa ya yi yunkurin kashe kansa saboda karancin albashi

Direban Aso Villa ya yi yunkurin kashe kansa saboda karancin albashi
Source: Depositphotos

An tattaro cewa lamarin ya afku ne a ranar Litinin bayan matar direban ta gano wata yar wasika da rubuta akan kisan da zai yi a kan teburinsu

Don haka sai tayi gaggawar sanar da makwabta abunda ke faruwa, don haka suka bazama nemansa.

An bayyana cewa direban ya daura yunkurin nasa akan karancin albashi a cikin wasikar da ya bari.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da babban sakataren majalisar dinkin duniya UN

Da aka kira shi akan wayar tarho Offre ya bayyana cewa sharrin shaidan ne ya rude shi har yayi yunkurin hallaka kansa.

Haka zalika da aka tuntubi sakataren din-din-din na fadar shugaban kasa, Mista Jalal Alabi wanda ya tabbatar da rahoton yace ya ziyarci direban a asibiti.

Yace kuma direban yayi danasanin aikata abun da yayi sannan ya shawarce shi da kada ya sake aikata hakan.

Kan karacin biyan, yace babu abunda fadar shugaban kasa zata iya yi cewa lamarin tarayya ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel