Jam’iyyu da-dama sun yi watsi da PDP sun bi bayan Jam'yyar APC a zaben Osun

Jam’iyyu da-dama sun yi watsi da PDP sun bi bayan Jam'yyar APC a zaben Osun

Mun samu labari daga Jaridar The Nation ta kasar nan cewa akalla Kananan Jam’iyyu 20 ne za su marawa Jam’iyyar APC baya a karashen zaben Jihar Osun da ake sa ran kammalawa yau dinnan.

Jam’iyu da-dama sun yi watsi da PDP sun bi bayan Jam'yyar APC a zaben Osun

Kananan Jam’iyyu sun nemi Magoya bayan su su zabi APC
Source: Original

Jam’iyu da-dama sun zabi su bi bayan APC a zaben Osun inda ake sa ran cewa yau za a zabi sabon Gwamna a Jihar. Jam’iyyun adawa karkashin ACPP sun tabbatar da cewa za su marawa APC baya a zaben da ake shirin gudanarwa yau Alhamis.

ACPP hadaka ce ta kananan Jam’iyyun adawa irin su ADC, APA, NCP, da PDC wanda su ka samu kuri’u da-dama a zaben da aka gudanar sun nuna cewa APC za su yi a zaben yau. Shugaban hadakar Adesoji Masilo ya bayyana wannan.

KU KARANTA: Zaben Osun: Cacar baki ya kacame tsakanin APC da PDP

Adesoji Masilo yayi magana a madadin sauran Jam’iyyun jiya a Garin Osogbo watau babban Birnin Jihar Osun inda ya tabbatar da cewa za su bi bayan Jam’iyyar APC domin ita ce Jam’iyyar da ke kokarin kawo cigaba a Jihar Osun.

Prince Masilo ya nemi mutanen su su zabi APC a zaben da za a karasa yau inda ya koka da yadda ake saida kuri’u a zaben. Jam'iyyun dai su na bayan Gboyega Oyetola wanda shi ne 'Dan takarar APC a matsayin Gwamnan Jihar Osun.

Jiya kun ji cewa ‘Dan takarar Jam’iyyar adawa ta SDP Iyiola Omisore ya marawa Jam’iyyar APC mai mulki baya a zaben da za a fafata tsakanin PDP da APC bayan ya gana da manyan APC jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel