Melania Trump za ta ziyarci Kasashen Ghana, Malawi, Kenya da Masar

Melania Trump za ta ziyarci Kasashen Ghana, Malawi, Kenya da Masar

Mun ji labari cewa Uwargidar Kasar Amurka Melania Trump ta shirya kai ziyara zuwa wasu Kasashen Afrika a zagayen da ta ke yi ita kadai ba tare da Mai gidan ta Shugaba Donald Trump ba.

Melania Trump za ta ziyarci Kasashen Ghana, Malawi, Kenya da Masar

Melania tayi watsi da Najeriya a ziyarar ta zuwa Afrika
Source: Depositphotos

Jaridun Turai da-dama sun rahoto cewa Uwargida Misis Melania Trump za ta ziyarci Kasashen da su ka hada da Ghana, Malawi, Kenya har da kuma Kasar Masar. Trump za ta ziyarci dai kowane bangare kenan na Nahiyar Afrikar.

Wannan ne karon farko da Melania Trump za ta sa kasa a Kasar Afrika kusan tun da ta shiga fadar Shugaban kasa. Trump ta bayyana wannan ne lokacin da ta gana da Matan Shugabannin Kasashen Afrika a wajen taron UN da ake yi.

KU KARANTA: Mataimakin Gwamnan Kano yace fetur ya sa Najeriya ta rabu da noma

A Ranar Litinin ne Mai dakin Shugaba Trump din za ta iso Nahiar Afrika domin kawo tsare-tsaren da za su taimaki kananan yara. Kungiyar nan ta USAID ce dai za ta ba Uwargidar Amurkar kwarin-gwiwar wannan tafiya da za tayi.

Matar Shugaban kasar ta Amurka za tayi kokarin kare kananan yara a Afrika daga matsalar kwayoyi da talauci da sauran su. Melania Trump ta dai gana da Matan Shugabannin kasashen na Ghana, Malawi da kuma Kenya jiya.

A karshen makon jiya kun ji cewa Aisha Buhari ta kama hanya zuwa Kasar Amurka domin wani babban taro a Majalisr Dinkin Duniya inda za su zauna game da kamuwa da cutar kanjamau a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel