Gwamnatin jihar Kwara ta amince da daukar malamai 1, 850 aiki a fadin jihar

Gwamnatin jihar Kwara ta amince da daukar malamai 1, 850 aiki a fadin jihar

- Gwamna Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara ya amince da daukar malamai 1,850 aiki, da zasu koyar a makarantun firamare da sakandire

- Malamai 1,500 da zasu yi aiki karkashin hukumar SUBEB yayin da sauran malaman 350 zasu koyar a makarantun sakandire

- Gwamnan jihar ya baiwa hukumar SUBEB da TSC umurnin bayar da sanarwar daukar aikin a kafofin watsa labarai

Gwamna Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara ya amince da daukar malamai 1,850 aiki, da zasu koyar a makarantun firamare da sakandire da ke a fadin jihar don cike gurbin karancin malamai da jihar ke fama da shi musamman a fannin darussan kimiyya tare da kuma samar da ayyukanyi a jihar.

A cewar wata sanarwa daga babban mai tallafawa gwamnan ta fuskar watsa labarai, Dr. Muyideen Akorede, da ya bayar a ranar Laraba, gwamnati ta yanke wannan hukunci ne sakamakon bukatun da hukumar ilimi bai daya ta jihar da kuma hukumar kula da harkokin malaman makarantun jihar Kwara suka gabatar na son karin ma'aikatan.

Gwamnatin jihar Kwara ta amince da daukar malamai 1, 850 aiki a fadin jihar

Gwamnatin jihar Kwara ta amince da daukar malamai 1, 850 aiki a fadin jihar

Akorede wanda ya ce hukumomin guda 2 sun gabatar da wannan bukatar tasu tare da kprafin rashin malamai da zasu koyar a darussan turanci dana kimiyya, ya kuma ce gwamnan ya amince da daukar malamai 1,500 da zasu yi aiki karkashin hukumar ilimi bai daya ta jihar SUBEB yayinda sauran malaman 350 zasu koyar a makarantun sakandire.

KARANTA WANNAN: Kungiyar ASUP a jihar Bauchi ba zasu bi sahun NLC wajen shiga yajin aikin kwanaki 7 ba

Akorede ya kara da cewa akwai karancin malamai a makarantun firmare da sakandire na jihar duk da daukar malamai aiki da gwamnatin jihar Kwara ta yi karkashin shirin bunkasa matasa KWAYEP da kuma malaman da aka dauka aiki a jihar karkashin shirin gwamnatin tarayya na N-Power.

Babban mai tallafawa gwamnan ya ce gwamnan jihar ya baiwa hukumar SUBEB da TSC umurni, da su bayar da sanarwar daukar aikin a kafofin watsa labarai, tare da bukatarsu akan bin matakan da suka dace yayin daukar aikin a gundumomi 193 da ke a fadin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel