Gwamnatin Tarayya da Jihohi sun gididdiba N741.84b a tsakanin su - FAAC

Gwamnatin Tarayya da Jihohi sun gididdiba N741.84b a tsakanin su - FAAC

A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnatin tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomin kasar nan suka kasafta tare da raba N741.84b a tsakanin su. Kudin shiga kenan da kasar nan ta samu a watan Agusta da ya samu doriya ta N20.04n kan N714.84 da suka raba a watan Yuli.

Sakataren dindindin na Ma'aikatar kudi ta kasa, Mahmoud Isa Dutse, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito.

Mista Dutse ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taron kwamitin gwamnatin tarayya kan kasafi da gididdiba kudi, inda yace an samu kari na kudaden shiga sabanin yadda aka samu a watan Yuli a sakamakon karuwar adadi na ma'adanan man fetur da Najeriya ta fitar domin sayarwa a kasashen ketare.

Gwamnatin Tarayya da Jihohi sun gididdiba N741.84b a tsakanin su - FAAC

Gwamnatin Tarayya da Jihohi sun gididdiba N741.84b a tsakanin su - FAAC
Source: Depositphotos

Legit.ng ta fahimci cewa, Najeriya ta fitar da adadin gangunan ma'adanan man fetur 37.4m a watan Yuli, inda kuma ta fitar da ganguna 45.7m a watan Agustan da ya gabata da hakan ya yi sanadiyar karuwa ta kudaden shiga da kasar nan ta tara.

KARANTA KUMA: Manema aikin Hukumar FRSC sun roki Gwamnatin tarayya kan kara iyakar shekarun haihuwa na daukan aiki

A yayin fayyace yadda gididdibar kudaden ta kasance, Sakataren ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samu N274.88b inda a kasafta N139.42b a tsakanin gwamnatocin jihohin kasar nan yayin da kananan hukumomi kuma suka tashi da N107.49b.

Kazalika, an kasafta N53.03b a tsakanin jihohi masu samar da man fetur a kasar nan da wannan adadi na kudi ya zamto kasho 13 cikin 100 na kudaden shiga da kasar ta samu na watan Agusta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel