Yaki da cin hanci: Fayose ya yiwa Buhari tambayoyi 8 masu wuyar amsawa

Yaki da cin hanci: Fayose ya yiwa Buhari tambayoyi 8 masu wuyar amsawa

A yayin da ya rage saura 'yan kwanaki ya mika mulki ga hannun zababben gwamnan jihar Ekiti, gwamna mai barin gado, Ayodele Fayose, ya yi wasu tambayoyi har guda 8 ga shugaba Buhari a kan yakin da gwamnatinsa ke yi da cin hanci.

Ga jerin tambayoyin 8 da Fayose ke fatan Buhari ya amsa masa.

1. Ina son mai girma shugaban kasa ya sanar da 'yan Najeriya yadda gwamnati tayi da dalar Amurka miliyan $43m da aka samu a ginin Osbourne Towers dake Ikoyi a jihar Legas

2. Me gwamnatinka tayi a kan zargin da ake yiwa shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPC), Maikanti Baru, na bayar da kwangila ta dalar Amurka miliyan $25m ba tare da bin ka'idoji ba?

3. Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta zargi shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu, da ministan shari'a, Abubakar Malami, da cin hanci. Me gwamnatinka tayi a kai?

Yaki da cin hanci: Fayose ya yiwa Buhari tambayoyi 8 masu wuyar amsawa

Buhari da Fayose
Source: Depositphotos

3. Me yasa har yanzu ba a bayyana waye ya mallaki ginin LEGICO shopping Plaza dake kan titin Ahmadu Bello a unguwar Victoria Island ta Legas inda hukumar EFCC tayi ikirarin ta samu dalar Amurka miliyan $448.8 a ciki ba?

5. Waye ya kawo miliyan N49m a cikin buhunhuna 5 da EFCC ta kama a filin jiragin sama na Kaduna?

DUBA WANNAN: Wata kungiya ta je har harabar majalisar dinkin duniya domin yiwa Buhari kamfen

6. Ina aka kwana a kan zargin karbar cin hancin miliyan N500m daga kamfanin sadarwa na MTN da ake yiwa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari?

7. Me ya faru da rahoton binciken badakalar mayar da Abdulrashid Maina bakin aiki da tuntuni aka mika maka?

8. Ko shugaban kasa na shirin yin amfani da tsintsiyar APC ne ya share takardun rahoton binciken Maina zuwa kwandon shara?

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel