Zaben fitar da 'yan takara: Oshiomhole ya yiwa shugabannin APC na jihohi gargadin karshe

Zaben fitar da 'yan takara: Oshiomhole ya yiwa shugabannin APC na jihohi gargadin karshe

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya gargadi shugabannin jam'iyyar na jihohi da su guji yin duk abinda zai nuna cewar suna goyon bayan wani dan takara.

Oshiomhole na wannan gargadi ne ga shugabannin a gabanin zaben fitar da 'yan takara da jam'iyyar zata fara yau, Alhamis, da kujerar shugaban kasa.

Shugaban ya yi wannan gargadi ne yayin mika rajistar 'yan jam'iyya ga shugabannin jihohi a jiya, Laraba, a Abuja.

Oshiomhole ya ce duk shugaban da aka samu da saba doka a jiharsa zai iya rasa kujerar sa ko kuma a saka masa takunkumi ko a ci tarar sa.

Zaben fitar da 'yan takara: Oshiomhole ya yiwa shugabannin APC na jihohi gargadin karshe

Adams Oshiomhole
Source: Depositphotos

Kazalika ya bukaci su kasance masu gaskiya a yayin gudanar da zabukan da kuma tabbatar da cewar basu yi kokarin canja rajistar mambobin jam'iyyar ko boye ta ba.

Oshiomhole ya kara da cewar uwar jam'iyyar APC zata tura da wakilai da zasu saka ido yayin gudanar da zabukan fitar da 'yan takarar a fadin jihohin kasar nan.

DUBA WANNAN: 2019: Wata kungiya ta je yiwa Buhari kamfen a majalisar dinkin duniya

Tun a kwanakin baya ne Legit.ng ta kawo maku labarin cewar a yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, shugabancin jam’iyyar APC na kasa ya amince da bukatar shugabancin jam’iyyar na jihohi tare da basu dammar amfani da hanyar da suke so domin gudanar da zabukan fitar da ‘yan takara, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

Legit.ng ta samu rahoton cewar APC ta yanke wannan shawara ne bayan ganawar fiye da sa’o’i uku da aka yi tsakanin shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, da gwamnonin APC 22 a gidan gwamnatin jihar Imo dake unguwar Asokoro a Abuja, a ranar Laraba ta makon jiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel