'Yan Bindiga sun sace masu hakar ma'adinai 16 a Kaduna - 'Yan sanda

'Yan Bindiga sun sace masu hakar ma'adinai 16 a Kaduna - 'Yan sanda

A yau, Laraba ne Hukumar 'Yan sanda na Jihar Kaduna ta tabbatar da sace wasu masu hakar ma'adinai 16 da wasu 'yan bindiga su kayi a karamar hukumar Birnin Gwari da ke Jihar.

A cewar 'yan sandan, masu hakar ma'adinan suna hanyarsu ta dawowa daga wajen hakar ma'adinai a cikin motansu ne 'yan bindigan su kayi musu kwantan bauna su kayi awon gaba da su.

Lamarin ya faru ne a Dajin Pole Wire da ke kusa da kauyen Bogoma da ke garin ne Birnin Gwari.

'Yan Bindiga sun sace masu hakar ma'adinai 16 a Kaduna - 'Yan sanda

'Yan Bindiga sun sace masu hakar ma'adinai 16 a Kaduna - 'Yan sanda

Kakakin hukumar 'yan sanda,Yakubu Sabo ya ce cikin wadanda aka sace har da wani Isa Tanimu da wasu mutane 15 duk 'yan gari daya.

DUBA WANNAN: Mutane 18 sun rasu sakamakon mummunan hatsarin mota da ta afku a hanyar Legas

Ya kuma ce hukumar ta aike da jami'anta domin su bi sahun 'yan bindigan amma a halin yanzu 'yan bindigan sun fara magana da iyalen wadanda suka sace suna tambayarsu kudaden fansa muddin sona son sake ganin 'yan uwansu.

Mr Sabo ya ce hukumar 'yan sandan za tayi iya kokarinta domin ganin ta ceto wadanda a kayi garkuwar da su.

Birnin Gwari dai gari ne da ya yi kaurin suna a jihar Kaduna saboda hare-haren da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane suka da de suna yi a yankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel