Najeriya za ta bayar da gudunmuwa wajen yakar Cutar Tarin Fuka a Duniya - Buhari

Najeriya za ta bayar da gudunmuwa wajen yakar Cutar Tarin Fuka a Duniya - Buhari

A ranar Larabar da ta gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari a can birnin New York na kasar Amurka, ya sake jaddada sadaukar da kai da jajircewa ta kasar Najeriya wajen yakar cutar Tarin Fuka a fadin duniya baki daya.

Cikin gabatar da jawabansa, Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin halartar wani babban taro kan tashi tsaye domin yakar cutar tarin fuka a fadin duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Buhari ya ziyarci kasar ta Amurka ne domin halartar taron majalisar dinkin duniya karo na 73 da ake gudanarwa kan wasu muhimman al'amurra da suka shafi kasashen duniya baki daya.

Buhari ya sha alwashin tsarkake Najeriya daga Cutar Tarin Fuka

Buhari ya sha alwashin tsarkake Najeriya daga Cutar Tarin Fuka
Source: Facebook

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, a yayin ziyarar sa shugaba Buhari ya kuma halarci wani taro na daban domin tattauna tsare-tsare da hanyoyin yakar tarin fuka sakamakon tasiri na barazanar wannan mummunar annoba ga lafiya, zamantakewa da kuma tattalin arziki.

KARANTA KUMA: Rayuka 9 sun salwanta a wani Mummunan Hatsari da ya auku a jihar Ekiti

Cikin wata sanarwa da sanadin kakakin shugaban kasar, Mista Femi Adesina ya bayyana cewa, wannan shine karo na farko da aka gudanar da wani gagarumin taro bisa ga manufa ta tashi tsaye domin yakar annobar tarin fuka.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta samu nasarar cafke wasu miyagun 'yan ta'adda 15 da suka shahara da muzgunawa al'ummar wasu yankuna dake jihar Sakkwato.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel