Matakin Omisore na marawa APC baya a zaben jihar Osun abun kunya ne - Femi Kayode

Matakin Omisore na marawa APC baya a zaben jihar Osun abun kunya ne - Femi Kayode

Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma babban jigo a jam'iyyar PDP, Chief Femi Fani-Kayode ya bayyana takaicinsa akan yadda ya yi amai ya lashe a lokaci daya, bayan da ya bayyana matakinsa na marawa jam'iyyar APC baya a zaben gwamnan jihar Osun karo na biyu da za a gudanar ranar Alhamis.

Tsohon ministan ya yi ikirarin cewa kwanaki biyu kafin sake zaben, dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar SDP, Omisore ya sha alwashin ci gaba da kasancewa a cikin takarar; sai dai abun takaici a cewar Kayode, dan takarar ya koma bayan APC don bata damar yin nasara a zaben gwamnan jihar.

A zaben gwamnan jihar na farko da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata, dan takarar PDP, Sanata Ademola Adeleke ya samu jimillar kuri'u 254,698, yayin da Oyetola Gboyega na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 254, 345, wanda ya tilasta hukumar INEC daukar matakin sake wani zaben saboda gaza yin zaben wasu kananan hukumomi.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Abraham Obasanjo ya jaddada goyon bayansa ga tazarcen shugaban kasa Buhari a 2019

Matakin Omisore na marawa APC baya a zaben jihar Osun abun kunya ne - Femi Kayode

Matakin Omisore na marawa APC baya a zaben jihar Osun abun kunya ne - Femi Kayode
Source: Depositphotos

Fani-Kayode wanda bai ji dadin wannan mataki na rana tsaka ba, a ranar Laraba ya bayyana cewa "matakin da Omisore ya dauka na goyawa APC baya a sake zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar Alhamis abun takaici ne. Wai ace zai hana Ile Ife ta samu kujerar mataimakin gwamna saboda kudi."

"Kwanaki biyu da suka gabata ya shaida mun cewa ba zai canja ra'ayinsa ba, haka zalika a jiya ya tabbatarwa ubanmu Baba Ayo Adebanjo cewa ba zai janye takararsa ba. Ban san abunda ya sa har ya sauya ra'ayinsa ba, amma mu zamu ci gaba, kuma zamu samu nasara da ikon Allah," a cewar Kayode.

Akwai rahotannin da ke cewa an samu musayar wasu makudan kudade a lokacin da wasy jiga jigan jam'iyyar APC suka ziyarci gidan Omisore da ke Ile Ife.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel