Raba gardama: Jihar Osun ta bayar da hutu saboda zabe

Raba gardama: Jihar Osun ta bayar da hutu saboda zabe

Gwamnatin Jihar Osun ta bayar da hutun kwana daya a ranar Alhamis 27 ga watan Satumban 2018 saboda gudanar da zaben raba gardama a jihar.

Sanarwan da ta fito daga bakin mai bawa gwamnan shawara na musamman kan kafafen yada, Sola Fasure, ta ce gwamnatin ta bayar da hutun ne saboda ma'aikatan gwamnati su samu sukunin zuwa su kada kuri'unsu.

Za'a gudanar da zaben ne a rumfunan zabe guda 7 a kananan hukumomi hudu a jihar.

Raba gardama: Jihar Osun ta bayar da hutu saboda zabe

Raba gardama: Jihar Osun ta bayar da hutu saboda zabe
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan majalisa 9 sun sauya sheka a wata jihar APC

Kananan hukumomin da za'a gudanar da zaben raba gardamar sun hada da Ife ta Kudu, Ife ta Arewa, Orolu da kuma Osogbo. Masu zabe 3,498 ne za su kada kuri'a zaben.

Baturen zabe na jihar, Joseph Fuwape, ya sanar ba'a kammala zaben ba a ranar Asabar saboda adadin kuri'un da ke tsakanin jam'iyyun da suka fi samun kuri'a ba ta kai yawan kuri'un da aka soke a kananan hukumomin ba.

Duk da cewa jam'iyyu 48 ne za su fafata a zaben, ainihin fafatawar yana tsakanin jam'iyyar APC ne da PDP.

Jam'iyyar SDP da ta zo ta uku a zaben tayi hadin gwiwa da jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel