Rayuka 9 sun salwanta a wani Mummunan Hatsari da ya auku a jihar Ekiti

Rayuka 9 sun salwanta a wani Mummunan Hatsari da ya auku a jihar Ekiti

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito za ku ji cewa, jini da hawaye sun kwaranya a garin Igede dake jihar Ekiti, yayin da rayukan mutane 9 suka salwanta a sanadiyar aukuwar wani hatsari da ya yi matukar munin gaske.

Baya ga mutane 9 da suka riga mu gidan gaskiya da sanyin safiyar ranar yau ta Laraba, akwai mutum guda da aukuwar hatsarin ta gadar ma sa munanan raunuka rai a hannun Mai Duka.

Rahotanni sun bayyana cewa, sassa da kuma gunduwa-gunduwar ta tsokar jikin dan Adam sun daidaita kan babbar hanyar Igede yayin da hatsarin ya auku da misalin karfe 6.15 na safiya daura da ofishin hukumar zabe ta INEC.

Aukuwar hatsarin ta hadar da wata karamar mota kirar Toyota Hiace mai lamba EKY 978 XJ da kuma wata babbar Mota kirar DAF mai lamba XB 404 FKA, inda nan take rayukan Mutane 9 suka salwanta ba bu ko shurawa.

Rayuka 9 sun salwanta a wani Mummunan Hatsari da ya auku a jihar Ekiti

Rayuka 9 sun salwanta a wani Mummunan Hatsari da ya auku a jihar Ekiti
Source: Depositphotos

Mutuwa da sanyin jiki ta kama mashaidan wannan mugun gani yayin da hawayen wasu daga cikin su ya kwaranya saboda tsanani na tausayi, inda tuni aka killace gawar wadanda ajali ya katsewa hanzari a dakunan ajiyar gawa dake asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake jihar.

KARANTA KUMA: An cafke masu garkuwa da Mutane 15 a jihar Sakkwato

Kakakin hukumar kula da manyan hanyoyi reshen jihar, Muhammad Olowo ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari tare da gargadin masu ababen hawa akan kiyaye dokoki a ka'idoji na sufuri.

Legit.ng ta fahimci cewa, tsautsayi da ba ya wuce ranarsa ya sanya wannan hatsari ya auku a sanadiyar tsala gudu da ya wuce misali daga bangaren direban karamar motar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel