An kama matashin dake yiwa rayuwar Atiku da iyalinsa barazana

An kama matashin dake yiwa rayuwar Atiku da iyalinsa barazana

- Hukumar 'yan sanda tayi bajakolin wani matashi da ya yi barazanar tarwatsa jirgin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar

- Matashin na amfani da wayar sata wajen aika sakonnin barazana ga Atiku, diyarsa da kuma matar sa

- Mai barazanar ya kware a yaren Turanci, Ibibio, Rasha da ma na kasar Portugal (Portuguese)

A yau, Laraba, ne hukumar 'yan sandan Najeriya tayi bajakolin wani mutum mai shekaru 43 dake barazana ga rayuwar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar matukar bai janye burinsa na son yin takarar shugaban kasa a shekarar 2019 ba.

A cewar kakakin hukumar 'yan sanda na kasa, Jimoh Moshood, wanda ake zargin mai suna, Augustus Akpan, na amfani da wayar sata ne wajen yin barazana ga Atiku, matar sa da kuma diyar sa.

An kama matashin dake yiwa rayuwar Atiku da iyalinsa barazana

Jimoh Moshood yayin bajakolin matashin dake yiwa rayuwar Atiku da iyalinsa barazana
Source: Depositphotos

Akpan, dan asalin kauyen Edemaya dake karamar hukumar Ikot Abasi a jihar Akwa Ibom, ya shiga hannun hukuma ne yayin da yake kokarin tserewa zuwa jihar Legas. An same shi da kudaden kasar waje masu yawa da ya damfari manyan mutane ta hanyar yin karyar cewar shi ma'aikacin hukumar leken asiri ta kasar Amurka (CIA) ne da hukumar tsaro ta kasar Amurka (FBI).

DUBA WANNAN: Guguwar canji: Tsohon gwamnan PDP a arewa ya tsallaka zuwa APC

Moshood ya kara da cewar mutumin ya kware a yaren Turanci, Ibibio, Rasha da na kasar Portugal (Portuguese). Sannan ya kara da cewa zasu cigaba da tsare shi har sai sun kammala bincike kafin su gurfanar da shi a gaban kotu.

A kwanakin baya ne Atiku ya yi korafin cewar ana yiwa rayuwar sa barazana saboda yana takarar shugaban kasa.

Akpan ya amsa laifinsa a jawabin da ya rubuta bayan an kama shi. Kazalika ya bayyana cewar ba wani dan siyasa yake yiwa aiki ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel