Gobara daga teku: Za a rufe kotuna karfe 12:00 na daren ranar Alhamis don afkawa yajin aiki

Gobara daga teku: Za a rufe kotuna karfe 12:00 na daren ranar Alhamis don afkawa yajin aiki

- Kungiyar JUSUN ta umurci mambobinta da su shiga yajin aiki kamar yadda kungiyar kwadago ta umurta

- Ana kuma sanar da dukkanin ma'aikatan fannin shari'a da cewar za a rufe kowace kotu da ke fadin kasar

- Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bayar da umurnin shiga yajin aikin gargadi a fadin kasar daga karfe 12:00 na daren Alhamis

Shuwagabannin kungiyar ma'aikatan fannin shari'a ta kasa JUSUN, da ke a inuwar uwar kungiyar ma'aikatan fannin shari'a na jihohi dana gwamnatin tarayya da ke fadin kasar, sun umurci dukkanin mambobinsu da su shiga yajin aiki kamar yadda kungiyar kwadago ta umurta don suma gwamnati ta cika masu akawarinsu na karin albashi.

Shugaban kungiyar JUSUN, Mr. Marwan Adamu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya bayar ranar Larabar nan, inda ya ce ma'aikatan fannin shari'ar za su shiga yajin aikin ne da misalin karfe 12:00 na daren ranar Alhamis, inda za rufe dukkanin kotunan da ke fadin kasar.

Ya bayyana cewa: "A matsayinmu na kungiyar da ta jingina da kungiyar kwadago ta kasa NLC, muna umurtar dukkanin mambobin kungiyarmu ta JUSUN da su yi zamansu a gidajensu daga daren ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba, 2018.

Gobara daga teku: Za a rufe kotuna karfe 12:00 na daren ranar Alhamis don afkawa yajin aiki

Gobara daga teku: Za a rufe kotuna karfe 12:00 na daren ranar Alhamis don afkawa yajin aiki
Source: UGC

KARANTA WANNAN: Tambuwal ya sha alwashin kawo karshen ta'addanci tare da sake gina Arewa maso Gabas

"Ana kuma umurtar dukkanin ma'aikatan fannin shari'a da su sani za a rufe kowace kotu da ke fadin kasar har sai anji sanarwar mataki na gaba daga babbar sakatariyar kungiyar ta kasa.

"An kafa wani kwamitin da ke aiki tare da hadin guiwar kungiyar NLC da kuma wasu masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa kowa ya bi wannan umurnin."

NAJ.com ta ruwaito maku cewa kungiyar hadakar kungiyoyin kwadago da suka hada da NLC, TUC da dai sauransu, sun bayar da sanarwar fara yajin aikin gargadi a daren ranar alhamis dinnan, sakamakon gazawar gwamnatin tarayya na kin amincewa da bukatunta na karawa ma'aikata albashi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel