2019: Buhari ne dan takarar shugaban kasa mafi cancanta – Tsohon hadimin Saraki

2019: Buhari ne dan takarar shugaban kasa mafi cancanta – Tsohon hadimin Saraki

Alhaji Moshood Mustapha, tsohon hadimin Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, yace dalilin dayasa ya abi ci gaba da zama jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne sabda ya yarda da iyawar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Mustapha ya bayyana haka ranar Laraba, 26 ga watan Satumba a wata hira da manema labarai a Ilorin.

Yayi bayanin cewa a matsayinsa na jagoran kungiyar kamfen din Buhari/Osinbajo a Kwara a 2015, bai shiya barin tafiyar ba a tsakiyar kogi da sunan tsira ba.

2019: Buhari ne dan takarar shugaban kasa mafi cancanta – Tsohon hadimin Buhari

2019: Buhari ne dan takarar shugaban kasa mafi cancanta – Tsohon hadimin Buhari
Source: Depositphotos

Mustapha wanda yayi aiki a matsayin kwamishina a karkashin Saraki yace ya yanke shawarar tsayawa da Shugaba Buhari saboda da yancin zabama kansa abunda yake ganin ya dace.

Ya kuma jadadda cewa cikin yan takarar dake neman kujeran shugabancin kasa kaf bai ga tamkar Buhari ba.

KU KARANTA KUMA: Gajiya ce ta sa ni barci a zauren Majalisar Dinkin Duniya – Gwamnan Edo

Daga karshe, Mustapha mai neman takarar kueran gwamnan jihar Kwara karkashin jam’iyyar APC yayi bayanin cewa ba zai iya saboda tsohon ubangidansa ya zama dan siyasar tashi ba da zai dunga tsalle daga jam’iyya guda zuwa wata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel