Tambuwal ya sha alwashin kawo karshen ta'addanci tare da sake gina Arewa maso Gabas

Tambuwal ya sha alwashin kawo karshen ta'addanci tare da sake gina Arewa maso Gabas

- Tambuwal, ya sha alwashin kawo karshen matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar tare da kuma sake gina jihohin yankin Arewa maso Gabas

- Ya yi ikirarin cewa gwamnati mai ci a yanzu ba ta tabuka komai wajen kawo karshen ta'addanci a kasar

- Tambuwal ya bukaci jami'an da za su kad'a kuri'a a PDP da su zabe shi a ranar babban taron jam'iyyar na fitar da gwanaye

Gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, ya sha alwashin kawo karshen matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar tare da kuma sake gina jihohin yankin Arewa maso Gabas da yakin 'yan tada kayar baya ya lalata idan har ya zama shugaban kasa a 2019.

Tambuwal ya bayyana hakan a lokacin ganawarsa da jami'an kad'a kuri'a a zaben fitar da gwani nda kuma mambobin jam'iyyar PDP a jihohin Borno da Yobe, taron da ya gudana a garin Maiduguri, babbar cibiyar da rikicin ya fi shafa.

Tambuwal ya yi nuni da cewa a lokacin da yake kan kujerar kakakin majalisar wakilai ta tarayya, jihohin da Arewa maso Gabas sun samu gagarumin taimako don kawo karshen matsalolin tsaro a yankin.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: A shirye na ke a gudanar da zaben fitar da gwani a jihar Legas - Ambode

Tambuwal ya sha alwashin kawo karshen ta'addanci tare da sake gina Arewa maso Gabas

Tambuwal ya sha alwashin kawo karshen ta'addanci tare da sake gina Arewa maso Gabas
Source: Facebook

Ya yi ikirarin cewa gwamnati mai ci a yanzu ba ta tabuka komai wajen kawo karshen ta'addanci a kasar, yana mai jaddada cewa jami'an tsaro da dama sun gamu da ajalinsu a hannun 'yan ta'addan, wanda gwamnati ba ta son bayyanawa.

"Da ikon Allah, zamu sake daukar kwararrun ma'aikata, mu kawo sabbin hanyoyin kimiya da fasa da zasu taimaka wajen kawo karshen rikice-rikicen da ake yi a yankin Arewa maso Gabas. Zamu kawo karshen halin fargabar da kasarmu take ciki," a cewarsa.

Gwamnan jihar Sokoton ya ce lokaci ya yi da za a sake gina makarantu, asibitoci, da kuma farfado da tattalin arzikin jihohin shiyyar.

"Zamu fi maida karfi wajen murkushe 'yan ta'addan da ke yankin tafkin Chadi. Sam bani da wata masaniya akan kokarin da gwamnati mai ci a yanzu ta ke yi na kawo karshen 'yan ta'addan da ke samun mafaka a tafkin chadi. Insha Allahu, zan tabbata tattalin arziki ya habbaka a Borno. Za a samar da ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya, makarantun zamani da na addini."

Tambuwal ya bukaci jami'an da za su kad'a kuri'ar da su zabe shi a ranar babban taron jam'iyyar PDP da za a gudanar don fitar da 'yan takara, da zai gudana 5 zuwa 6 ga watan Oktoba, a garin Fatakwal, jihar Rivers.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel