Zaben Jihar Osun: APC za ta hada-kai da Omisore ta lallasa PDP

Zaben Jihar Osun: APC za ta hada-kai da Omisore ta lallasa PDP

Dazu nan labari ya zo mana cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta samu hadin gwiwar ‘Dan takarar Jam’iyyar SDP Iyiola Omisore wajen doke PDP a karashen zaben Osun da za ayi gobe Alhamis.

Zaben Jihar Osun: APC za ta hada-kai da Omisore ta lallasa PDP

Omisore wanda yake da karfi a Yankin da za a sake zabe zai goyi bayan APC
Source: Facebook

Iyiola Omisore da Jam’iyyar sa ta SDP za ta marawa Jam’iyyar APC mai mulki baya ne a zaben da za ayi gobe inda za a fafata tsakanin PDP da APC. Hakan na zuwa ne bayan Shugaban APC Adams Oshimhole ya gana da Omisore.

Omisore ya fadawa manema labarai a Garin Ile Ife cewa zai yi aiki da APC bayan Jam’iyyar ta amince za ta tafi a kan muradun Jam’iyyar su ta SDP. ‘Dan takarar yace irin wannan sharadi ne ya gindayawa Jam’iyyar PDP mai adawa a baya.

KU KARANTA: A shirye na ke a gudanar da zaben fitar da gwani a APC - Ambode

Adams Oshimhole ne da wasu Gwamnoni da manyan kusoshin Jam’iyyar APC su ka kai wa Sanata Iyiola Omisore ziyara su na neman ya dafa nasu wajen ganin sun samu nasara a kan tsohuwar Jam’iyyar sa ta PDP a karashen zaben gobe.

Daga cikin sharudan da ‘Dan takarar ya bugawa APC akwai biyan albashi a kan kari tare da biyan bashin da jama’a ke bi na watanni da zarar an hau mulki. Har wa yau Iyiola Omisore ya nemi a gina abubuwan more rayuwa a Jihar Osun.

Jam’iyyar SDP dai ta samu kuri’a fiye da 120, 000 a zaben da aka yi a makon can. Jam’iyyar PDP da kuma APC dai sun yi kan-kan-kan ne. Sanata Iyiola Omisore yayi Mataimakin Gwamna a Jihar sannan kuma ya nemi Gwamna a PDP a 2014.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel