Yajin aikin gama-gari: Muna da mai na wata guda ne kacal - NNPC

Yajin aikin gama-gari: Muna da mai na wata guda ne kacal - NNPC

- Matatar man fetur ta kasa tace PMS na kwanaki 37 ya rage a fadin kasar

- An ja kunnen masu ababen hawa da kada suyi ta siyan man suna adanawa

- Gwamnatin tarayya tana iya kokarin ta gurin kawo karshen yajin aikin

Yajin aikin gama-gari: Muna da mai na wata guda ne kacal - NNPC

Yajin aikin gama-gari: Muna da mai na wata guda ne kacal - NNPC
Source: UGC

Matatar man fetur ta kasa tace kwanaki 37 ya rage PMS wanda aka fi sani da fetur ya kare karkaf a kasar.

Matatar ta bayyana haka ne a wata takarda da mai magana da yawun ta yasa hannu, Mista Ndu Ughamadu, a ranar laraba a garin Abuja.

Yace manajan daraktan matatar, Dr. Makanti Baru, ya roki masu ababen hawa da sauran masu amfani da fetur da kada su tsorata su dinga siyan man suna boyewa saboda yajin aikin da kungiyar kwadago ta kasa ta fara.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya zarce kawai, samarin kasar nan

Yace Gwamnatin tarayya tana iya kokarin ta gurin sulhuntawa da kungiyar kwadago. Ughamadu yace man fetur wanda zai isa Najeriya na kwanaki 37 ya rage a kasar.

Ya tabbatar da cewa duk wasu rassan matatar dake kasar, da kuma wadanda matatar ta yarje ma wa gurin siyar da mai zasu cigaba da siyar da kayayyakin man fetur domin amfanar yan kasa.

Matatar ta kara da cewa zata cigaba da tabbatar da cewa yan Najeriya na samu ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel