Shugaban NUJ ya sha alwashin kawo gyara a kafafen sada zumunta

Shugaban NUJ ya sha alwashin kawo gyara a kafafen sada zumunta

- Ana amfani da kafafen don yada labaran karya

- Abin ya kai har hukumomi na kama masu wannan laifi

- Shugaban NUJ ya sha alwashin magance matsalar

Shugaban NUJ ya sha alwashin kawo gyara a kafafen sada zumunta

Shugaban NUJ ya sha alwashin kawo gyara a kafafen sada zumunta
Source: UGC

Shugaban kungiyar 'yan jarida na kasa watau NUJ, Malam Abdulwaheed Odinsile, a yau laraba a Kano, ya sha alwashin hada kai da masu samar da layuka na yanar gizo dake bada damar yada labaran karya, dasu zage su kawo karshen lamarin.

A ziyarar da ya kai jihar Kanon, yaje ne da zimmar neman goyon bayan 'yan kungiyar, kan yadda zasu mara masa baya don sake neman zaben shugabancin kungiyar, karo na biyu.

A cewarsa, marasa aikin yi, da ma masu son yada shirme kan hau yanar gizo don kawai su baza labaran karya, wanda kan rudar da lamarin asalin labarai na gaskiya.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya zarce kawai, samarin kasar nan

A kalamansa: "Kakkabe irin wadanan gurbatattu na da wahala sosai, amma muna iya kokarinmu, kuma wannan yasa muke neman hada kai da kafaen dake samar da hanyoyin sadarwas ta zamani, don ganin an magance matsalar kacokan".

Labaran karya dai kan saurin yaduwa fiye da mma na gaskiya, wanda wasu lokutan kan jawo tashin hankulla a yankunan kasa, musamman a annnin kabilanci da siyasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel