Da dumi dumi: A shirye na ke a gudanar da zaben fitar da gwani a jihar Legas - Ambode

Da dumi dumi: A shirye na ke a gudanar da zaben fitar da gwani a jihar Legas - Ambode

- Mr. Akinwunmi Ambode, ya jaddada cewa baya tsoron fafatawa a zaben fitar da gwani na kujerar gwamnan Legas

- APC a jihar Legas ta shirya gudanar da zaben fitar da gwani a ranar Asabar ta hanyar kato bayan kato

- Gwmanan ya roki al'ummar jihar da su sake zabarsa don zarcewa kamar yadda suka zabe shi a 2015

Gwamnan jihar Legas, Mr. Akinwunmi Ambode, ya jaddada cewa zai shiga cikin masu takara a zaben fitar da gwani na kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC da za a gudanar a ranar Asabar. Tsarin kato bayan kato za a bi don kad'a kuri'ar zaben fitar da gwani a jihar.

A cikin wata sanarwa daga kwamishin watsa labarai na jihar, Mr. Kehinde Bamigbetan, gwamnan ya ce ba zai juya baya ga hukuncin da shuwagabannin jam'iyyar na Legas suka yanke ba, ko kuma bijirewa matsayar majalisar mashawartan gwamnan na tsayawa takara da kuma amincewa da zaben fitar da gwani ta hanyar kato bayan kato.

A yayin da jam'iyyar APC ta shirya gudanar da zaben fitar da gwani a ranar Asabar, 29 ga watan Satumba, 2018 ta hanyar kato bayan kato, gwamnan ya ce a shirye ya ke ya fuskanci sauran yan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar tunda dai ya mayar da fom din tsayawa takara tare da kaddamar da yakin zabensa don neman tazarce a shugabancin jihar.

KARANTA WANNA: An kafa sabuwar kotun hukunta duk jami'in sojin da aka kama ya sa hannu a zaben 2019 - Buratai

Da dumi dumi: A shirye na ke a gudanar da zaben fitar da gwani a jihar Legas - Ambode

Da dumi dumi: A shirye na ke a gudanar da zaben fitar da gwani a jihar Legas - Ambode
Source: Depositphotos

Gwamnan ya jinjinawa shugaban jam'iyyar na kasa, dattawa da kuma mambobin majalisar zartaswa, dama kafatanin mambobin jam'iyyar ta APC musamman al'ummar jihar Legas da suka bashi goyon baya a zaben 2015, da kuma fatan za su sake bashi hadin kai don ci gaban jihar a zaben 2019.

Sanarwar ta kara da cewa a kokarin da gwamnan ya ke yi na neman tazarce, ya fara tuntubar iyaye da kuma mambobin jam'iyyar da ke a jihar, cikin ladabi da nuna girmamawa tare da bukatarsu akan sake bashi dama don hada kan jihar da zummar zamanta jihar 'yan uwa daya.

Ta kara da cewa baiwa gwamna Ambode dama a karo na biyu zai tabbatar da dorewar bunkasar tattalin arzikin jihar; tabbatar da bunkasar walwala da jin dadin al'ummar jihar da kuma tabbatar da cewa ba a samu wata wariya a jihar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel