Yanzu Yanzu: Kotu ta ba da umurnin sakin shugaban PDP, Diekola

Yanzu Yanzu: Kotu ta ba da umurnin sakin shugaban PDP, Diekola

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa wata babban ktun Oshogbo a rana Laraba, 26 ga watan Satumba, ta umurci rundunar yan sanan Najeriya da ta saki wani jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party, Fatai Oyedele Diekola da wasu biyu dake tsare.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Justis A.O Ayoola bayan wani korafi da aka shigar kan Diekola; Sikiru Lawal da Segun Adekilekun.

Yanzu Yanzu: Kotu ta ba da umurnin sakin shugaban PDP, Diekola

Yanzu Yanzu: Kotu ta ba da umurnin sakin shugaban PDP, Diekola
Source: Depositphotos

Rahotannin sun kuma nuna cewa kwafin takardan na a Osogbo inda tsohon kwamishinan bayanai, Sunday Akere, wanda ya kasance abokin Diekola ya gabatar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa an kara tsakanin magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da na Peoples Democratic Party (PDP) kan zargin wani yunkuri da yan siyasa suka yin a siyan katin zabe gabannin zaben gwamna da za’a sake gudanarwa a wasu kananan hukumomin jihar Osun a ranar Alhamis, 27 ga watan Satumba.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa rikicin ya barke ne bayan wani jigon PDP, Fatai Oyedele, wanda aka fi sani da Diekola ya jagoranci wasu shugabannin jam’iyyar zuwa mazaba ta 17 a ward 5 a Alekuwodo kan zargin siyan katin zabe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Rikici a gidan Kwankwasiyya, Farfesa Hafiz yayi fito-na-fito da Kwankwaso, zai yi takaran gwamna

An tattaro cewa yan sanda sun kama jigon na PDP kan zargin haka, amma jam’iyyar tan ace kan cewa yana kamfen don samun kuri’u ne ba wai siyan katin zabe ba kamar yadda ake zargi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel