An kafa sabuwar kotun hukunta duk jami'in sojin da aka kama ya sa hannu a zaben 2019 - Buratai

An kafa sabuwar kotun hukunta duk jami'in sojin da aka kama ya sa hannu a zaben 2019 - Buratai

- Tukur Buratai, ya ce an kafa sabuwar kotun da za ta ladabtar da jami'an sojin da aka kama su sa hannu a zaben 2019

- Ya yii nuni da cewa duk wani jami'in sojin da ya ke ganin yana da sha'awar siyasa, to ya ajiye aikinsa don bin ra'ayin zuciyarsa

- Haka zalika an haramtawa jami'an soji gudanar da ibadu a waje, sai a wuraren da aka ware a cikin bariki

Hafsan rundunar sojin kasa, Laftanar Tukur Buratai, ya ce an kafa sabuwar kotun da za ta rinka ladabtar da jami'an sojin da aka kama suna taimakawa wasu yan siyasa, a ci gaba da fusknatar babban zaben 2019.

Buratai wanda ya bayyana hakan a ranar Talata ya ce biyo bayan kafa wannan kotun, ya zama wajibi ga shuwagabannin sansanonin soji da kuma kwamandoji da su gargadi na kasa da su, don gujewa shiga harkokin siyasa ko kungiyoyin kabilu a fuskantar zaben 2019.

Hafsan sojin ya yi nuni da cewa duk wani jami'in sojin da ya ke ganin yana da sha'awar siyasa, to ya ajiye aikinsa don bin ra'ayin zuciyarsa ko zuciyarta.

Buratai ya yi wannan maganar ne a wani taron jami'an soji na 2 da na 3 da aka hada su a lokaci daya, ya kuma ce akwai bukatar kowanne jami'i ya gujewa rabar yan siyasa, wadanda ka iya neman tallafinsu a zaben 2019.

Buratai ya jaddata daukar hukunci akan duk wani jami'in soji da aka kama da shiga harkokin siyasa

Buratai ya jaddata daukar hukunci akan duk wani jami'in soji da aka kama da shiga harkokin siyasa
Source: Twitter

Ya ce: "A yayin da muke ci gaba da fuskantar zaben 2019, ya zama wajibi manyan jami'an soji da kuma kwamandoji su gargadi na kasa da su ko jami'an da ke karkashin kulawarsu akan kauracewa shiga harkokin siyasa, tare da tunasar da su dokokin zama a cikin inuwar sojin kasa.

"A matsayinmu na kwararrun sojoji, bai dace ace muna taimakawa wasu yan siyasa ba, ko kungiyoyin addinai da na kabilu. Duk wani jami'in sojin da ke sha'awar siyasa, yana da damar ajiye aikinsa don bin zabin zuciyarsa.

"Haka zalika an haramtawa jami'an soji gudanar da ibadu a waje, sai a wuraren da aka ware a cikin bariki, har sai idan wadanda aka baiwa izinin yin hakan bisa wasu kwararan hujjoji. Ina so in kara tabbatar maku da cewa kotun ladabtar da soji da aka kafa, za ta fara aiki na take," a cewar Buratai

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel