Yajin aikin dindindin: An goga gemu da gemu tsakanin Ministan kwadago da kungiyoyin kwadago

Yajin aikin dindindin: An goga gemu da gemu tsakanin Ministan kwadago da kungiyoyin kwadago

Da tsakar ranarnan ana can ana goga gem da gemu takanin kungiyoyin kwadago da suka kunshi kungiyar ma’aikata, NLC da kungiyar yan kasuwa, TUC a gefe daya da kuma gwamnatin Najeriya, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Idan za’a tuna Legit.ng ta ruwaito hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa ta umarci kafatanin ma’aikatan Najeriya dasu shiga yajin aikin gargadi na kwana biyu akan batun biyan sabon tsarin albashina naira dubu hamsin da shida (56,000).

KU KARANTA: Abin dariya: Gwamnan Najeriya ya bige da barci a yayin taron majalisar dinkin duniya

Kwatsam sai ga shi a ranar Laraba 26 ga watan Satumba kungiyar ta fitar da sabon sanarwar inda take umartar dukkanin ma’aikata, makarantu, bankuna, da duk wasu wuraren aiki walau na gwamnati ne ko na kudi dasu fara yajin aikin dindindin watau sai baba ta ji.

Kungiyar kwadagon ta bayyana daanganta dalilinta na shiga yajin aikin da biris da gwamnati ta yi da ita tun bayan karewar wa’adin kwanaki goma sha hudu da gindaya ma gwamnatin, don haka ta yanke shawarar shiga wannan yajin aiki har sai an biya ma’aikata sabon tsarin albashi.

Haka zalika NLC ta zargi gwamnati ta kin zama da kwamiti mai sassa uku da ta kafa dake tattauna yiwuwar kaddamar da tsarin sabon albashin, tare da kuma jan kafa da alamun ‘ba zai yiwu ba’ da gwamnatin ke nunawa.

Babbar bukatar NLC shine gwamnati ta tabbatar da sabon karancin albashi daga naira dubu goma sha takwas (18,000) zuwa naira dubu hamsin da shida (N56,000) saboda a cewarta farashin komai ya tashi a Najeriya, don haka ya kamata albashin ma’aikata ya karu.

Ana sa rai a yayin wannan zama ministan kwadago, Chris Ngige zai shawo kan kungiyar kwadago daga fadawa wannan yajin aiki da ka iya gurgunta komai a kasarnan, sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba’a kammala zaman tattaunawar ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel