Yanzu Yanzu: Omisore ya fada ma magoya bayansa wanda zasu zaben gwamnan Osun da za’a sake yi

Yanzu Yanzu: Omisore ya fada ma magoya bayansa wanda zasu zaben gwamnan Osun da za’a sake yi

Dan takarar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben gwamnan jihar Osun, Iyiola Omisore ya fada ma magoya bayansa da su zabi jam’iyyar siyasar da suke ganin za su yi masu abunda jam'iyyarsa ta nanadar masu.

A wani yunkuri na son gaje magoya bayansa, Omisore ya zanta da jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) bayan hukumar INEC ta kaddamar da cewa ba’a kammala zaben gwamnan jihar Osun ba.

A cewar Sahara Reporters, APC na shirin ba shi matsayin minister kan goyon bayansa a zaben da za’a sake a ranar Alhamis, 27 Satumba.

Yanzu Yanzu: Omisore ya fada ma magoya bayansa wanda zasu zaben gwamnan Osun da za’a sake yi

Yanzu Yanzu: Omisore ya fada ma magoya bayansa wanda zasu zaben gwamnan Osun da za’a sake yi
Source: Depositphotos

Sai dai a wata sanarwa daga Jide Fakorede, hadiminsa, Omisore ya yanke shawarar cewa ba zai sasanta don son zuciyarsa ba sannan ya yasar da mutanensa ba.

KU KARANTA KUMA: 2019: PDP na iya ajiye yan takarar kujeran shugaban kasa dake fuskantar shari’a

Saboda haka ya umurci magoya bayansa da su zabi duk jam’iyyar da suke ganin zasu yi masu abunda su yan SDP ke shirin yi masu wanda suka hada da: Shuganci mai inganci, ayyukan cigaba da sauransu.

Yace a matsayinsa na mai kishin damokradiyya dole ya ba mutane yancin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel