Abin dariya: Gwamnan Najeriya ya bige da barci a yayin taron majalisar dinkin duniya (UN)

Abin dariya: Gwamnan Najeriya ya bige da barci a yayin taron majalisar dinkin duniya (UN)

Gwamnatin jahar Edo ta mayar da martani ga wasu hotuna dake yawo a shafukan sadarwar yanar gizo dake nuna gwamnan jahar Godwin Obaseki yana sharara barci abinsa a yayin da shuwagabannin duniya ke tattaunawa a babban taron majalisar dinkin Duniya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito barcin ya kwashe gwamnan ne a daidai lokacin da shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ke gabatar da jawabinsa a yayin taron na majalisar dinkin Duniya karo na 73 daya gudana a birnin New York na kasar Amurka.

KU KARANTA: Rundunar Yansandan jahar Kano ta tarwatsa wasu gungun yan fashi da suka addabi jama’a

Abin dariya: Gwamnan Najeriya ya bige da barci a yayin taron majalisar dinkin duniya (UN)

Abin dariya
Source: Depositphotos

Sai dai kaakakin Gwamna Obaseki Crusoe Osagie ya gwamnan yayi barcin ne sakamakon gajiya da yayi kamar yadda duk wani dan adam ke gajiya, don haka wannan ba wani abin kunya bane saboda yana faruwa ga kowa.

“An janyo hankulanmu game da wani aikin abokan hamayya da suke kokarin bata ma gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki suna ta hanyar watsa wasu hotunan gwamnan yana barci a yayi taron majalisar din duniya,

“Babu wani magana a wannan hoto saboda gwamnan tare da sauran yan rakiyar shugaban kasa sun shafe awanni da dama a jirgi akan hanyarsu ta zuwa kasar Amurka, haka zalika kafin tafiyartasa gwamnan bai samu runtsawa ba a Najeriya saboda tarin ayyukan daya gabatar a ofishinsa.” Inji shi.

Abin dariya: Gwamnan Najeriya ya bige da barci a yayin taron majalisar dinkin duniya (UN)

Abin dariya
Source: UGC

Daga karshe Crusoe yace ko a yanzu idan za’a duba za ga hotunan manyan shuwagabannin kasashen Duniya yayin da uke barci a taron majalisar dinkin Duniya, don haka ba akan Miagidansa farau ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel