Ya aka iya: Ba dole kowane Likita sai ya zama kwararre a Najeriya ba - Adewole

Ya aka iya: Ba dole kowane Likita sai ya zama kwararre a Najeriya ba - Adewole

- Ministan lafiya ya nemi wasu Likitocin Najeriya su koma noma da dinki

- Isaac Adewole yace babu wanda yace dole ne sai kowa ya kware a asibiti

Ya aka iya: Ba dole kowane Likita sai ya zama kwararre a Najeriya ba - Adewole

Ministan lafiya yace wasu Likitoci za su kare a siyasa da noma
Source: Facebook

Mun samu labari dazu cewa Ministan lafiya Farfesa Isaac Adewole ya nuna cewa dole sai wasu Likitoci sun buge da harkar siyasa ko noma ko wata sana’ar domin su samu na abinci a Najeriya saboda halin da ake ciki a kasar nan.

Ministan kasar ya fito yace ba dole kowane Likita sai ya zama kwararre a Najeriya a dalin karancin Makarantun kara sanin aiki da ake da su ba. Don haka ne Adewole yace dole wasu su hakura su koma wasu sana’o’in dabam.

KU KARANTA: An kara samun wani Sojan Najeriya ya harbe kan sa da kan sa

Isaac Adewole yayi wannan jawabi ne a lokacin da aka yi masa tambaya game da karancin wuraren koyon aiki da ake da su a kasar wanda hakan ya sa masu son su kara gogewa a fannin lafiya su ke fama kwarai da gaske a Najeriya.

Ministan yace babu yadda za ace dole sai kowane Likita ya kware don haka abin da yace shi ne sai wasu su rungumi siyasa ko aikin noma ko kuma dinkin tufafi. Ministan yace karshen-karewa ma mai dinka masa kwat din zuwa ofis Likita.

Wannan kalamai da aka ji daga bakin babban Ministan na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sun batawa Jama’a rai. Yanzu dai kusan babu wadanda su ke fita zuwa Kasar waje domin samun albashi mai tsoka kamar Likitocin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel