Alkalin Kotu ya yanke ma wani dan luwadi hukunci mai tsanani bayan ya yi ma yaro fyade

Alkalin Kotu ya yanke ma wani dan luwadi hukunci mai tsanani bayan ya yi ma yaro fyade

Wata kotun majistri dake zamanta a garin Jos na jahar Filato ta yanke ma wani matashin dan luwadi mai suna Aliyu Ibrahim tsatstsauran hukunci bayan ta kama shi da laifin yi ma wani karamin yaro dan shekara goma fyade, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito alkalin kotun, Jovita Binjin ta yanke ma Aliyu dan luwadi mai sana’ar facin taya hukunci ne a ranar Larahba, 26 ga watan Satumba, inda tace ta kama shi da laifuka biyu da suka shafi fyade.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya rarraba ma makarantun Firamari sabbin babura 107

Shi dai wannan hukunci mai tsanani da Alkali Binjin ta yanke ma Aliyu ya kunshi zaman gidan yari na tsawon watanni ashirin da biyu (22), tare da horo mai tsanani, ko kuma ya biya taran kudi naira dubu ashirin (N20,000)

Da take yanke hukunci, Alkali Binjin tace tana fatan wannan hukunci ya zama darasi ga sauran masu sha’awar aikata wannan laifi, a farkon zaman Kotun ne dai dansanda mai kara, Tawel Ijubtil ya bayyana ma Kotu cewa a ranar 15 ga watan Agusta ne wani mai suna Haruna Aliyu ya kai musu kara.

Dansandan yace wanda ake kara ya sha zakke ma yaron a duk lokacin daya tafi makaranta, sa’annan yayi masa barazanar kashe shi idan har ya sake ya fada ma iyayensa ko wani.

Da wannan ne dansandan yace wannan laifi da ake tuhumar matashin ya saba ma sashi na 284 da na 399 na kundin hukunta manyan laifuka na yankin Arewacin Najeriya. Allah ya kare nagari da mugu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel