Ni na dauko Ganduje na daura kan mulki a Jihar Kano - Inji Kwankwaso

Ni na dauko Ganduje na daura kan mulki a Jihar Kano - Inji Kwankwaso

- Kwankwaso yace shi ya dauko Ganduje ya sa ya zama Magajin sa

- Sanatan yace Ganduje ya gaza don haka dole aka ja daga a Kano

- Yace ya dauko Ganduje a 2015 ne domin cigaban Kwankwasiyya

Ni na dauko Ganduje na daura kan mulki a Jihar Kano - Inji Kwankwaso

Sanata Rabiu Kwankwaso yace shi ne silar zaman Ganduje Gwamna
Source: Depositphotos

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa shi ne silar zaman Ganduje Gwamnan Jihar Kano a 2015. Yanzu dai an ja layi tsakanin Ganduje da tsohon Mai gidan na sa na fiye da shekaru 8 a siyasa.

A makon nan ne Rabiu Kwankwaso ya ziyarci Jihar Kano ba tare da Jama'a sun ankara ba. Sanatan yace shi ne yayi ruwa da tsarin wajen ganin Ganduje ya dare kujerar da ya bari ganin shi ne Mataimakin sa na shekara da shekaru.

KU KARANTA: Saraki na gab da tafiya kurkuku idan bai yi wasa ba

Kwankwaso yace yayi hakan ne domin Kwankwasiyya ta zauna lafiya uwa daya uba daya. Tsohon Gwamnan yace da ace ba Ganduje ya tsaida a 2015, da Gandujen yayi bore a tafiyar Kwankwasiyya domin shi ne gaba da kowa a lokacin.

Injiniya Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa a halin yanzu Ganduje ya gaza sannan kuma yayi watsi da tafarkin Kwankwasiyya tuni don bai yi amfani da tsarin girma ba. Kwankwaso yace wannan ya sa dole su ka ja daga ya tsaida 'Dan takarar sa.

A makon nan dai tsohon Gwamnan na Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana abin da ya sa ya tsaida Abba Kabir Yusuf a matsayin ‘Dan takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel