'Yan majalisa 9 sun sauya sheka a wata jihar APC

'Yan majalisa 9 sun sauya sheka a wata jihar APC

- 'Yan majalisar jihar Oyo 9 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar African Democratic Congress ADC

- Cikin wadanda suka sauya shekar har da mataimakin kakakin majalisar jihar, Abdulwasi Musah

- A halin yanzu APC na da 'yan majalisa 18, ADC na da 12 sannan PDP tana da mambobi biyu kacal

'Yan majalisa 9 sun fice daga APC a jihar Oyo

'Yan majalisa 9 sun fice daga APC a jihar Oyo
Source: UGC

'Yan majalisar jihar Oyo 9 ciki har da Mataimakin Kakakin majalisar jihar, Abdulwasi Musah sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyun APC, Accord Party da Labour Party zuwa jam'iyyar African Democratic Congress ADC a jihar.

Biyar daga cikin 'yan majalisar sun fice daga APC ne, uku kuma sun fice daga Accord Party sai guda daya ya fice da Labour Party kuma duk suka dunguma zuwa African Democratic Congress ADC.

DUBA WANNAN: Na fitar da tsammanin zabe na adalci a gwamnatin Buhari - Dan takarar PDP

Magatakardan Majalisar, Paul Bankole ne ya karanto wasikar sauya shekar na su zuwa ADC a zauren majalisar a zaman da akayi a jiya Talata.

Bayan mataimakin Kakakin majalisar, Sauran wanda suka sauya shekan sune Lukman Balogun, Bolaji Badmus, Azeez Billiaminu, Ganiyu Oseni, Olusegun Olaleye, Samson Oguntade da Muideen Olagunju.

Ficewar wadanda 'yan majalisar ya kawo adadin mambobin ADC a majalisar zuwa 12 yayin da jam'iyyar APC mai mulki tana da mambobi 18, ita kuma jam'iyyar PDP tana da mambobi 2 kacal.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel