Zaben 2019: Dattawan PDP sun soma shirin fito da dan takara 1 da zai kara da Buhari

Zaben 2019: Dattawan PDP sun soma shirin fito da dan takara 1 da zai kara da Buhari

- Dattawan PDP sun soma shirin fito da dan takara 1 da zai kara da Buhari

- Sunce suna da yakinin samun sulhu a tsakanin su

Babban kwamitin amintattu na jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP), ya ce tuni yayi nisa wajen ganin ya kwantar da dukkan wata fitina da ka iya tasowa zaben fitar da gwanin dan takarar jam'iyyar na shugaban kasa a ranar 6 ga watan Okotoba mai zuwa.

Zaben 2019: Dattawan PDP sun soma shirin fito da dan takara 1 da zai kara da Buhari

Zaben 2019: Dattawan PDP sun soma shirin fito da dan takara 1 da zai kara da Buhari
Source: Depositphotos

Shugaban kwamitin amintattun, Sanata Walid Jibrin shine ya sanar da hakan a garin Abuja, ranar Litinin din da ta gabata inda ya bayyana cewa kawo yanzu dai suna ta kokarin ganin 'yan takarar dukkan su sun amince da sasancin da zai fito da mutum daya a tsakanin su.

Legit.ng dai ta samu cewa jam'iyyar ta Peoples Democratic Party (PDP) yanzu haka tana da jumlar jama'a sha biyu da suka nuna sha'awar su ta tsayawa takarar shugaban kasa a inuwar ta da kuma suka sayi fom din takarar.

Idan dai ba'a manta ba manya daga cikin masu neman takarar karawa da shugaba Buhari da ke zaman dan takarar jam'iyyar APC daya tilo sun hada da Atiku Abubakar, Sanata Kwankwaso, Sule Lamido, Gwamna Dankwambo da Tambuwal da dai sauran su.

A wani labarin kuma, Yanzu haka dai ma'aikatan gwamnati da masu karbar fansho a jihar Benue dake a yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya na cikin zullumi da bakin ciki biyo bayan labarin kwace kudaden da shugaba Buhari ya baiwa jihar a watan jiya.

Kudaden dai wadanda majiyar mu ta tabbatar mana da cewa na biyan rankon nan ne da ake cewa 'Paris Club', gwamnatin tarayya ta baiwa jihar kason ta na sama da Naira biliyan 14 domin su biya ma'aikata albashin da suke bin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel