Abubuwa 5 da shugaba Buhari yayi magana kan su a majalisar dinkin duniya

Abubuwa 5 da shugaba Buhari yayi magana kan su a majalisar dinkin duniya

Shugaban kasar tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari dai yanzu haka yana birnin New York dake a can kasar Amurka inda yake halartar taron shugabannin kasashen duniya karo na 73.

Taron dai na kasashen duniya, kamar yadda muka samu majalisar dinkin duniya ce kan shirya shi a duk shekara inda akan tattauna akan al'amurran da suka shafi kasashe daban-daban.

Legit.ng ta samu cewa a wannan shekarar ma, shugaban kasar ya halarci taron kuma ma a gabatar da jawabi a wajen ranar Talatar da ta gabata kuma ga wani tsakure da muka yi maku game da abubuwan da ya yi magaba akan su.

Abubuwa 5 da shugaba Buhari yayi magana kan su a majalisar dinkin duniya

Abubuwa 5 da shugaba Buhari yayi magana kan su a majalisar dinkin duniya
Source: Depositphotos

1. Ta'addanci

Buhari yayi magana kan yadda ta'addanci yake ta kara mamaye duniya da kuma irin kashe kashen da hakan ke jazawa a kasashe irin su Yamen, Siriya da ma Boko Haram. Ya kuma yi kira da a hadu domin kawo karshen hakan.

2. Rikicin makiyaya da manoma

Shugaban kasar ta Najeriya ya kuma yi magana akan yadda rikici tsakanin manoma da makiya yake ta kara yawaita a duniya tare da kira a kawo karshen matsalar.

3. Matsalar bakin haure

Shugaba Buhari ya kuma yi magana agame da matsalar bakin haure inda ya danganta lamarin da rashin kykkyawar rayuwa a wasu sassan duniya inda ya bukaci taimakon kasashe masu arziki don kawo karshen matsalar.

4. Yaki da cin hanci da rashawa

Haka zalika shugaban kasar yayi magana akan matsalar cin hanci da rashawa da yadda ta ke addabar kasashen Afrika da ma sauran kasashe masu tasowa.

5. Matsalar sauyin yanayi

A nan ma shugaban kasar yayi jawabi mai tsawo akan yadda ya kamata dukkan kasashe su maida hankali wajen shawo kan matsalar dumamar yanayi dake matukar barazana ga al'umma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel