Mutane 18 sun rasu sakamakon mummunan hatsarin mota da ta afku a hanyar Legas

Mutane 18 sun rasu sakamakon mummunan hatsarin mota da ta afku a hanyar Legas

- Wata motan fasinjoji tayi hatsari a hanyar Legas zuwa Abuja

- Dukkan fasinjoji 17 da direban motan sun rasu sakamakon karo da su kayi ta traila

- Hatsarin ya afku ne a karamar hukumar Irepodun/Ifelodun da ke jihar Ekiti a safiyar yau

Mutane 18 sun rasu sakamakon mummunan hatsarin mota da ta afku a hanyar Legas

Mutane 18 sun rasu sakamakon mummunan hatsarin mota da ta afku a hanyar Legas

Mun samu daga Vanguard cewar fasinjoji 18 ne suka rasa rayyukansu a safiyar yau a garin Awo da ke karamar hukumar Irepodun/Ifelodun da ke jihar Ekiti sakamakon wata mummunan hatsarin mota.

DUBA WANNAN: Na fitar da tsammanin zabe na adalci a gwamnatin Buhari - Dan takarar PDP

An ruwaito cewa motar kirar Toyata Hiace ta dauko fasinjojin ne daga Legas inda suka nufi Abuja amma sai su kayi karo da wata Traila a garin Awo - Igede a safiyar yau Laraba.

Shaidan ganin ido ya tabbatar da cewa dukkan mutanen da ke cikin motar sun rasu sakamakon take su da tirelan ya yi wand hakan ya sa motar ta yi lakume tare da su a cikinta.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa Rundunar Operation Lafiya na Sojin Najeriya da ke aikin samar da zaman lafiya a Arewa maso Gabas sunyi nasarar ceto mutane 73 tare da lalata wata mabuyar 'yan Boko Haram a wata samamen tsakar dare da suka kai a Sirdiwala da ke Borno.

Sojojin kuma sunyi nasarar halaka mayakan Boko Haram 7 tare da kwato wasu makamai duk a harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel