Ta-leko-ta-koma: Shugaba Buhari ya kwace Naira biliyan 14.9 din da ya ba wata jihar Arewa

Ta-leko-ta-koma: Shugaba Buhari ya kwace Naira biliyan 14.9 din da ya ba wata jihar Arewa

- Shugaba Buhari ya kwace Naira biliyan 14.9 din da ya ba wata jihar Arewa

- Yanzu haka ma'aikatan jihar na cikin zullumi

Yanzu haka dai ma'aikatan gwamnati da masu karbar fansho a jihar Benue dake a yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya na cikin zullumi da bakin ciki biyo bayan labarin kwace kudaden da shugaba Buhari ya baiwa jihar a watan jiya.

Ta-leko-ta-koma: Shugaba Buhari ya kwace Naira biliyan 14.9 din da ya ba wata jihar Arewa

Ta-leko-ta-koma: Shugaba Buhari ya kwace Naira biliyan 14.9 din da ya ba wata jihar Arewa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Gwamnan Osun ya fadi ta cikin sa bayan sakamakon zabe

Kudaden dai wadanda majiyar mu ta tabbatar mana da cewa na biyan rankon nan ne da ake cewa 'Paris Club', gwamnatin tarayya ta baiwa jihar kason ta na sama da Naira biliyan 14 domin su biya ma'aikata albashin da suke bin su.

Legit.ng ta samu cewa sai dai kuma daga baya labari ya baza gari cewa ana shirin kwace kudin bayan da gwamnan ya umurci ma'aikatar harkokin kudin jihar da ta soma biyan ma'aikata bashin albashin su.

A jihar dai ta Benue, wasu ma'aikatan na cikin garagi inda akan samu ba'a biya su albashi ba na tsawon watanni da dama.

A wani labarin kuma, Kimanin kwanaki uku kacal a shiga zaben fitar da gwani 'yan takarar gwamnonin jahohi a karkashin inuwar jam'iyya mai mulki a Najeriya ta APC, gwamnan Borno, Kashim Shettima ya zabi wanda yake so ya maye gurbin sa.

Wanda dai gwamnan ya bayyana goyon bayan sa a gare shi shine Farfesa Babagana Umara Zulum dake zaman kwamishinan gyara da kuma sake tsugunnar da wadanda ibtila'in ta'addancin Boko Haram ya shafa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel