Daga karshe: Gwamnan Borno ya zabi wanda yake so ya zama magajin sa

Daga karshe: Gwamnan Borno ya zabi wanda yake so ya zama magajin sa

- Gwamnan Borno ya zabi wanda yake so ya zama magajin sa

- Ya zabi Farfesa Babagana Zulum

- Yanzu haka dai shi kwamishinan sa ne

Kimanin kwanaki uku kacal a shiga zaben fitar da gwani 'yan takarar gwamnonin jahohi a karkashin inuwar jam'iyya mai mulki a Najeriya ta APC, gwamnan Borno, Kashim Shettima ya zabi wanda yake so ya maye gurbin sa.

Daga karshe: Gwamnan Borno ya zabi wanda yake so ya zama magajin sa

Daga karshe: Gwamnan Borno ya zabi wanda yake so ya zama magajin sa
Source: Getty Images

KU KARANTA: Sojin sama sun illata 'yan Boko Haram

Wanda dai gwamnan ya bayyana goyon bayan sa a gare shi shine Farfesa Babagana Umara Zulum dake zaman kwamishinan gyara da kuma sake tsugunnar da wadanda ibtila'in ta'addancin Boko Haram ya shafa.

Legit.ng ta samu cewa wannan dai ya biyo bayan ziyarar da wata tawagar shugabannin gargajiya da wasu dattawan jihar suka kai masa tare da gabatar masa da bukatar su a kan hakan.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa kusan sama da mutum ashirin ne suka nuna sha'awar su ta zama yan takarar gwamna a jam'iyyar APC a jihar ta Borno.

A wani labarin kuma, Mahaifiyar 'yar makarantar nan ta Dapchi da har yanzu take a hannun 'yan ta'addan, Lear Sharibu da suka sace ta a watannin baya, mai suna Rebecca Sharibu ta shigar da kara a kotu tana neman diyyar Naira miliyan 500 akan batan diyar ta ta.

Kamar yadda muka samu, mahaifiyar dalibar a cikin karar da ta shigar ta bukaci kotu ta tilastawa shugaba Buhari, ministan shari'a kuma Antoni Janar na gwamnatin tarayya, Abubakar Malami da kuma Insifekta Janar na 'yan sandan Najeriya su biya ta diyyar ta saboda sakacin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel