Gwamna El-Rufai ya rarraba ma makarantun Firamari sabbin babura 107

Gwamna El-Rufai ya rarraba ma makarantun Firamari sabbin babura 107

A kokarin na inganta harkar ilimi gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya kaddamar da rabon sabbin babura guda dari ga bakwai ga hukumomin kula da ilimin fimari dake kananan hukumomi ashirin da uku, 23.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnatin ta raba baburan ne da nufin samun kulawa a bangaren makarantun Firamari daga jami’an hukumomin, bugu da kari hakan zai basu damar kurdawa lungu lungu sako sako duk inda makarantun suke a fadin jahar.

KU KARANTA: Abubuwa 4 da zasu taimaka ma Nuhu Ribadu a takararsa ta gwaman jahar Adamawa

Gwamna El-Rufai ya rarraba ma makarantun Firamari sabbin babura 107

Babura
Source: Facebook

Haka zalika gwamnan yayi haka ne don rage ma Malaman makarantun wahalhalun ababen hawa, musamman wadanda suke karkara tare da inganta wuraren daukan karatu, gwamnan ya kara da cewa gwamnatin jahar Kaduna na aiki tukuru don inganta ilimi a jahar Kaduna.

Dayake jawabinsa a lokacin da yake mika baburan ga sakatarorin ilimi guda 23, shugaban hukumar ilimi ta bai daya, Malam Nasir Umar ya bayyana cewa manufar gwamnatin jahar Kaduna itace samar da ingantaccen ilimi ga jama’anta don haka ake ta samun garambawul a harkar.

Gwamna El-Rufai ya rarraba ma makarantun Firamari sabbin babura 107

Babura
Source: Facebook

Haka zalika yayi kira ga sakatarorin ilimi na jahar dasu tabbata sun raba baburan ga malamai da kuma jami’an da suka cancanta, domin a cewarsa da haka ne za’a samu karin kwarin gwiwa daga wajen Malaman wanda hakan zai sa su zage su yi aiki tukuru wajen ilimantar da yayanmu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel