Yan fansho uku da Buhari ya yiwa abin mamaki

Yan fansho uku da Buhari ya yiwa abin mamaki

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ya yi wani abin mamakin da mutanen Najeriya basu taba zato ba kuma wanda ya canza rayuwan yan fanshon da na iyalansu bayan sun fidda tsammani.

Legit.ng ta kawo muku wadannan yan fansho da wannan gwamnati ta biya bayan shekaru aru-aru da rike musu kudi.

1. Biyan kudin fanshon soji da yan sandan Biyafara

A ranan Laraba, 7 ga watan Oktoba 2017, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin biyan kudin fanshon yan sandan Biyafara da aka yafe laifukansu a shekarar 2000.

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ne ya yafe musu amma yaki cika alkawarin biyan kudin fanshonsu.

2. Ya biyan fanshon tsaffin ma’aikatan yan sanda, kwastam, hukumar shiga da fice, hukumar kurkuku, da ma’aikata na tsawon watanni 81

KU KARANTA: Uwargida ta kashe diyar kishiyarta da fiya-fiya

A ranan 4 ga watan Nuwamba 2016, gwamnatin tarayya ta bada umurnin biyan tsaffin ma’aikatan hukumar yan sanda, kwastam, hukumar shiga da fice, hukumar kurkuku, da ma’aikata kudin fanshon watanni 81 cikin watanni 87 da suke bin gwamnati tun lokacin da aka kara musu albashi.

3. Kudin fanshon tsaffin ma’aikatan jirgin saman Nigeria Airways

Sama shekaru 15 yanzu da kashe kamfanin Nigeria Airways, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin biyan tsaffin ma’aikatan kamfanin fanshonsu na N22.68 billion. Wannan kasha 50 cikin 100 na kudin da suke bin gwamnati ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel