Wasu ministoci a gwamnatin Shugaba Buhari sun samu sabani a tsakanin su

Wasu ministoci a gwamnatin Shugaba Buhari sun samu sabani a tsakanin su

- Wasu ministoci a gwamnatin Shugaba Buhari sun samu sabani a tsakanin su

- Ministocin sune na sufuri da na yada labarai

- Sun samu sabani ne game da kamfanin sufurin jirgin saman Najeriya

Karamin ministan sufuri a bangaren zirga-zirgar jiragen sama na kasa Sanata Hadi Sirika a firar da yayi da manema labarai ya bayyana cewa kamfanin sufurin nan na jirgin sama mallakin Najeriya watau 'Nigerian Air' da yanzu haka aka dakatar bai taba rasa masu sa hannun jari ba.

Wasu ministoci a gwamnatin Shugaba Buhari sun samu sabani a tsakanin su

Wasu ministoci a gwamnatin Shugaba Buhari sun samu sabani a tsakanin su
Source: Facebook

KU KARANTA: Sabon rikici ya barke a tsakanin ya'yan jam'iyyar PDP

Wannan dai na zaman tamkar martani ga ministan yada labarai na gwamnatin tarayyar, Alhaji Lai Mohammed da farko ya shaidawa 'yan Najeriya cewa rashin masu saka jari ne musabbabin dalilin dakatar da kaddamar da kamfanin.

Legit.ng ta samu cewa Sanata Hadi Sirika ya cigaba da cewa cikin wadanda suka nuna sha'awar su ta saka hannun jari a kamfanin akwai kamfanoni da dama daga fadin duniya kamar su Afro-Exim Bank, African Development Bank da kuma Standard Chartered Bank.

Mai karatu dai zai iya tuna a cikin satin da ya gabata ne ministan na sufuri ya bayyana cewa an dakatar da kaddamar da kamfanin na sufuri sakamakon wasu shirye-shirye da ba'a kammala ba

A wani labarin kuma, Mahaifiyar 'yar makarantar nan ta Dapchi da har yanzu take a hannun 'yan ta'addan, Lear Sharibu da suka sace ta a watannin baya, mai suna Rebecca Sharibu ta shigar da kara a kotu tana neman diyyar Naira miliyan 500 akan batan diyar ta ta.

Kamar yadda muka samu, mahaifiyar dalibar a cikin karar da ta shigar ta bukaci kotu ta tilastawa shugaba Buhari, ministan shari'a kuma Antoni Janar na gwamnatin tarayya, Abubakar Malami da kuma Insifekta Janar na 'yan sandan Najeriya su biya ta diyyar ta saboda sakacin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel