Zaben Osun: Cacar baki, da zarge zarge ya kacame tsakanin jam’iyyun APC da PDP

Zaben Osun: Cacar baki, da zarge zarge ya kacame tsakanin jam’iyyun APC da PDP

Cacar baki, nuna ma juna yatsa da murza gashin baki ya kaure tsakanin manyan jam’iyyun kasarnan, jam’uyyar APC da na PDP a yayin da ake gaba da gudanar zaben maimaici a zaben gwamnan Osun da aka fara a satin data gabata.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Alhamis, 27 ga watan Satumba ne hukumar zabe mai zaman kanta za ta karkare zaben da aka fara a ranar Asabar sakamakon ba’a samu sakamakon da zai tabbatar da nasarar jam’iyyar PDP dake kan gaba ba, ko na APC dake binta a baya.

KU KARANTA: BAbubuwa 4 da zasu taimaka ma Nuhu Ribadu a takararsa ta gwaman jahar Adamawa

Sai dai a wani sabon salo na rikicin siyasa, APC da PDP na zargin junansu da cewa tana hada katin zaben na daban da nufin amfani dasu wajen maguda sakamakon zaben, kamar yadda kowannensu ta tabbatar a ranar Talata 25 ga wata.

Shugaban jam’iyyar PDP, Soji Adagundo ne ya fara yin zargin a yayin wata ganawa da yan jaridu a garin Osogbo, inda yace: “APC na hada katin zabe a fadar gwamnatin jaha don su maguda zaben ranar Alhamis, haka zalika suna sayen katin zaben jama’a akan naira dubu hamsin zuwa dubu dari.

“Hakazalika INEC na sayar ma APC katin zaben da ba’a karba ba akan kudi naira dubu uku uku don su samu damar yin magudin zabe, bugu da kari a kokarinta na kwace nasarar PDP, APC ta hada kai da jami’an tsaro don su kai ma wasu daga cikin yayanmu hari

“Daga cikin wadanda suka kai ma hari akwai Alhaji Ashafa, Idowu Agbaje, da wasu jiga jigan yayan jam’iyyar PDP, don kuwa ko da safennan sai da yan daban APC suka yi barazana ga magoya bayanmu, amma ina jaddada musu babu wanda ya isa ya kwace nasararmu.” Inji ta.

Sai dai kaakakin jam’iyyar APC ta kasa, Yekini Nabenaya ya bayyana cewa sun samu wasu rahotanni daga majiyoyi nagartattu cewa jam’iyyar PDP na can tana harhada katin zabe na bogi da don su karbe jahar Osun daga hannuta kota halin kaka, don haka yayi kira ga INEC data binciki wannan zargi.

A zaben da aka buga a ranar Asabar, dan takarar PDP, Ademola Adeleke ya samu kuri’u 256, 698, yayin daGboyega Oyetola na APC ya samu kuri’u 254 345, sai dai nasarar Adeleke bata tabbata ba saboda bambamcin dake tsakaninsa da APC 353 ne yayin da kuri’un da aka soke sun kai 3,498, kuma dokar ta hana kuri’un da suka raba su yi kasa wadanda aka soke, don haka za’a maimaita zabe a inda aka soke.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel