2019: Buhari ne fitilar da zai haskaka Najeriya - Oyegun

2019: Buhari ne fitilar da zai haskaka Najeriya - Oyegun

- Tsohon Ciyaman din APC, John Odigie Oyegun ya ce Buhari ne fitilar da ke haska Najeriya a halin yanzu

- Oyegun ya ce babu wani dan takara a Najeriya da ya fi shugaba Buhari cancanta ya jagoranci Najeriya a wannan halin da kasar ta tsinci kan ta

- Oyegun ya ce Buhari na da nakusa a matsayinsa na dan adam amma duk da haka shine mafi dacewa a yanzu

Tsohon Ciyaman din jam'iyyar APC na kasa, Cif John Odigie Oyegun ya ce shugaba Muhammadu Buhari shine dan takarar da ya fi cancanta ya cigaba da jan ragamar mulkin Najeriya a zaben 2019.

A hirar da ya yi da manema labarai jiya a Benin ta jihar Edo, Oyegun ya ce a kasar da babu gwanaye Buhari ne ya cacanci ya cigaba da jagorancin kasar saboda halayensa na gaskiya da rikon amana.

2019: Buhari ne dan takara mafi cancanta - Oyegun

2019: Buhari ne dan takara mafi cancanta - Oyegun
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Na fitar da tsammanin zabe na adalci a gwamnatin Buhari - Dan takarar PDP

"Buhari ne fitilar da ke haskaka Najeriya a irin wannan lokacin da rashawa da cin hanci ta mamaye sassa daban-daban na kasar. Sai dai kamar ko wane dan adam, Buhari yana da nakasunsa amma a yanzu shi muke bukata domin Najeriya ta cigaba da bunkasa." inji shi

Da ya yi tsokaci kan zaben gwamna ta jihar Osun, Oyegun ya yabawa INEC kan yadda ta bawa al'umma damar zaban wanda suke so domin haka ne kawai za'a tabattar da samuwar demokradiyya mai dorewa.

A game da yaki da rashawa na gwamnatin Buhari, Oyegun ya ce APC ba ta hana hukumomin tsaro bincikar mutanen da suka dawo APC ba domin shuga jam'iyyar ba kariya bane ga wadanda ake tuhuma da aikata laifi.

Ya ce rashin samun shugabanci na gari, rashawa da cin hanci da rashin da'a ne suka janyo tabarbarewar abubuwa a Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel