Yan siyasan a jihar Kebbi na siyawa yan baranda makamai gabanin zaben 2019 – Hukumar Yan Sanda

Yan siyasan a jihar Kebbi na siyawa yan baranda makamai gabanin zaben 2019 – Hukumar Yan Sanda

Kwamishanan yan sandan jihar Kebbi, Ibrahim Kabiru, a jiya ya kawo kuka bisa yadda wasu yan siyasa a jihar suke baiwa yan daba muggan makamai gabanin zaben shugaban kasa, gwamnoni da yan majalisa a shekarar 2019.

Shugaban yan sandan jihar ya ce rahoton leken asirin da suka samu ya nuna cewa ana shirin amfani da wadannan makamai wajen kashe abokan hamayya.

Yayinda yake jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki kan yadda za’a gudanar da zaben 2019 cikin zaman lafiya a jihar, ya lashi takobin cewa duk wanda aka kama zai fuskanci fushin hukuma.

KU KARANTA: Uwargida ta kashe diyar kishiyarta da ‘Fiya-fiya’

Yace: “Rahoton leken asiri ya bayyana cewa wasu yan siyasa a jihar suna baiwa yan daba kudade domin siyan makamai irin takubba, wukake, gwafa da wasu muggan makamai da ka iya kawo hallakan abokan hamayya.”

Yace duk dan siyasan da aka kama da daukan nauyin wadannan matasa za’a hanasu takaran zabe sannan a cisu tara N500,000 ko aikasu kurkukun watanni 12.

A cewarsa: “Yan takara da jam’iyyun siyasa su nisanci maganganu ko jawabai lokacin yakin neman zabe da ka iya nuna cin mutunci ga abokan adawansu.”

Kwamishanan ya jaddada cewa wanda aka kama zai fuskanci fushin hukuma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel