Akwai yiwuwar Najeriya za ta sake tsunduma cikin matsin tattalin arziki - CBN

Akwai yiwuwar Najeriya za ta sake tsunduma cikin matsin tattalin arziki - CBN

Kwamitin Kula da Hauhawar Kudade na babban bankin Najeriya CBN tayi gargadin cewa alkalluman da suke bayyana yanzu a kan tattalin arzikin Najeriya na nuna cewa kasar za ta iya sake tsundumawa cikin matsin tattalin arziki.

Najeriya ta fice daga cikin matsin tattalin arzkin ne a shekarar 2017 bayan kwashe tsawon wattanni ana fama da matsalar kamar yadda kwamitin ta fadi a jiya Talata.

Akwai yiwuwar Najeriya za ta sake tsunduma cikin matsin tattalin arziki - CBN

Akwai yiwuwar Najeriya za ta sake tsunduma cikin matsin tattalin arziki - CBN
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Na fitar da tsammanin zabe na adalci a gwamnatin Buhari - Dan takarar PDP

A yayin da ya ke jawabi ga manema labarai bayan kammala taron kwanaki biyu da ya yi da mambobin kwamitin kula da hauhawar kudin a hedkwatan CBN da ke Abuja, gwamnan CBN, Mr Godwin Emefiele ya ce tattalin arzikin ya fara nuna alamun tabarbarewa.

Ya ce dalilan da suka janyo wannan tabarbarewan suna da alaka ne da fanin samar da man fetur na Najeriya inda aka samu ragowar daukan mutane aiki da bunkasar kasuwanci.

Sauran dalilan da ya lissafo sun hada da rashin fara aiki da kasafin kudin 2018, rashin kara albashi mafi karanci, ambaliyar ruwa da ya lalata gonakin manoma, rikicin makiyaya da manoma, matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Gabas da kuma karin basusukan kasashen waje.

Kwamitin ta shawarci gwamnati ta cigaba da aiwatar da kasafin kudin 2018 kana ta duba hanyoyin magance ambaliyar ruwa da ke adabar al'umma a kowanne shekara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel