Sake zaben Osun: Omisore ya hadu da Oshiomhole, gwamnonin APC, ya amince da yiwa jam’iyya mai mulki aiki

Sake zaben Osun: Omisore ya hadu da Oshiomhole, gwamnonin APC, ya amince da yiwa jam’iyya mai mulki aiki

Dan takarar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben gwamna da akayi a ranar 22 ga watan Satumba a jihar Osun, Cif Iyiola Omisore ya amince da yin aiki tare da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben da za’a sake gudanarwa a ranar Alhamis, 27 ga watan Satumba.

Legit.ng ta tattaro cewa an kulla yarjejeniyar ne bayan wats gsnses tdsksnin Cif Omisore da wasu manyan tawagar APC karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole a Osogbo a ranar Laraba, 26 ga watan Satumba.

Har ila yau cikin tawagar akwai Gwamna Abiola Ajimobi na Oyo, Gwamna Badaru Abubakar na Jigawa, Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano da Gwamna Ibikunle Amosun na Ogun.

Sake zaben Osun: Omisore ya hadu da Oshiomhole, gwamnonin APC, ya amince da yiwa jam’iyya mai mulki aiki

Sake zaben Osun: Omisore ya hadu da Oshiomhole, gwamnonin APC, ya amince da yiwa jam’iyya mai mulki aiki
Source: Facebook

Sauran sun hada da gwamna mai jiran gado; Dr Kayode Fayemi, ministan bayanai, Alhaji Lai Mohammed da mataimakin kakakin majalisar wakilai; Alhaji Yusuf Lasun.

KU KARANTA KUMA: Mata sun yi gangami game da shigar su harkar siyasa a Kano (hotuna)

A baya Legit.ng ta rahoto cewa jam’iyyar APC mai mulki ta zargi jam’iyyar adawa ta PDP da yunkurin yin magudi a zaben raba gardama da za a yi ranar Alhamis a jihar Osun, APC t ace PDP na buga katunan zabe na bogi ta hanyar yin amfani da sahihan bayanan dake kan katin masu zabe.

APC ta bayyana hakan ne ga Legit.ng ta hanyar wani jawabi da sakatarenta na yada labarai, Mista Yekini Nabena, ya fitar.

Nabena ya bayyana cewar APC ta tabbatar da hakan ta hanyar samun sahihan bayanan daga mambobinta dake sassan jihar Osun da za a maimaita zaben gwamna ranar Alhamis mai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel