2019: Manyan kalubale guda 4 dake barazana ga tazarcen gwamnan jahar Kaduna

2019: Manyan kalubale guda 4 dake barazana ga tazarcen gwamnan jahar Kaduna

Guda daga cikin gwamnonin yankin Arewacin Najeriya da kujerarsa ke rawa shine gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai sakamakon wasu sauye sauye da aka samu a jahar Kaduna a karkashin jagorancinsa.

A ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2015 ne aka rantsar da El-Rufai a matsayin gwamnan jahar Kaduna, inda tsohon gwamnan jahar, Muntari Ramalan ya mika masa ragamar mulki bayan ya lashe zaben a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Karshen tika tika tik: Gwamna Kashim Shettima ya fatattaki kwamishinoninsa

Sai dai Legit.ng ta ruwaito akwai wasu abubuwa da suka faru a jahar Kaduna, wadanda masana harkokin siyasa ke ganin abubuwan zasu iya kawo ma gwamnan jahar barazana game da burinsa na zarcewa akan kujerarsa. Daga cikinsu akwai;

2019: Manyan kalubale guda 4 dake barazana ga tazarcen gwamnan jahar Kaduna

Gwamnan jahar Kaduna
Source: UGC

1- Hawansa mulke keda wuya sai gwamnan ya fara karyawa da Malaman makaranta, inda ba tare da wata wata bay a fatattaki kimanin Malaman makarantun Firamari dubu ashirin da biyu (22,000), wadanda gwamnatin jahar ta bayyanasu a matsayin wadanda basu da igancin koyarwa

2- Haka zalika gwamnan jahar Kaduna ya koka game da yawan ma’aikatan dake kananan hukumomin jahar 23, inda yace yawancin ma’aikatannan basu da aikin yi a ma’aikatun, don haka kananan hukumomi basa iya biyansu albashi, hakan tasa ya sallami sama da ma’aikata dubu hudu daga kananan hukumomi.

3- Baya ga Malamai da ma’aikata, gwamnan jahar Kaduna yayi zargin hakimai da dagatocin jahar Kaduna sun yi yawa, yawan da ya kai gwamnati bata iya biyansu albashi, don haka gwamnan ya bukaci ya mayar da adadin hakiman zuwa yadda suke kafin shekarar 2003, hakan tasa ya sallami hakimai da dagaci dagaci da dama.

4- Matsala ta hudu dake yi ma tazarcen Gwamnan jahar Kaduna barazana itace rashin kammala ayyuka da dama daya faru a jahar, tun daga gyaran hanyoyi, gina sababbin hanyoyi, gayaran makarantu, musamman aikin kwatan da aka fara a jahar aka tsaya, da sauran ayyukan daya fara bai gama ba, wanda haka yasa jama’an garin Kaduna ke kokawa, inda wasu ke ganin gara su kawo wani sabon gwamnan da zai kammala duk aikin da ya fara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel