Ma’aikatan Najeriya za su fara yajin aiki

Ma’aikatan Najeriya za su fara yajin aiki

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa kungiyar Kwadago a Najeriya ta sanar da shiga yajin aiki daga karfe 12 na daren ranar Laraba 26 ga watan Satumba.

Kungiyar ma'aikata ta NLC da ta TUC sun sha alwashin daukar wannan mataki ne a wata sanarwar daga shugabannin kungiyoyin.

A sanarwar dauke da sa hannun babban sakataren NLC, Dr Peter Ozo-Eson, ya ce kwamitin koli na kungiyar sun zauna sati biyu da suka shige.

Ma’aikatan Najeriya za su fara yajin aiki

Ma’aikatan Najeriya za su fara yajin aiki
Source: Depositphotos

Kungiyar ta yi na’am da a sanar wa gwamnatin Tarayyar Najeriya cewa ma'aikata za su fara yajin aiki, idan ba’a duba lamarin sabon albashi mafi karanci na ma’aikatan kasar ba.

KU KARANTA KUMA: Ni zan yi nasara a Zaben 2019 - Tambuwal ya gargadi Shugaba Buhari

A nata bangaren kungiyar TUC ma ta shaidawa 'yan Najeriya ta hannun Mista Musa-Lawal Ozigi, sakatarenta na kasa, wanda ya bayyana aniyar kungiyarsu ta dakatar da dukkan ayyuka har sai gwamnatin Najeriya ta biya masu bukata.

Sanarwar ba ta bayyana lokacin da da za’a janye yajin aikin ba, sai dai ta yi nusar da 'ya'yan kungiyar da su tabbatar da an dakatar da ayyukan gwamnati a fadin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel