Ni zan yi nasara a Zaben 2019 - Tambuwal ya gargadi Shugaba Buhari

Ni zan yi nasara a Zaben 2019 - Tambuwal ya gargadi Shugaba Buhari

Mun samu cewa Gwamnan jihar Sakkwato kuma daya daga cikin manema tikitin takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Aminu Waziri, ya yi bugun gaba tare da cika baki na samun nasara a babban zabe na 2019.

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnan ya bayyana cewa, zai yi galaba akan shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin babban zaben mai ci gaba da karatowa.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Tambuwal ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyin manema labarai a farfajiyar babban ofishin jam'iyyarsa ta PDP dake birnin Minna na jihar Neja.

Tambuwal yake cewa, ya na da duk wata cikakkiyar cancanta ta hambare shugaba Buhari daga kujerarsa, wanda ya misalta shi da shugaba maras wayewa ta fuskar zamani.

Ni zan yi nasara a Zaben 2019 - Tambuwal ya gargadi Shugaba Buhari

Ni zan yi nasara a Zaben 2019 - Tambuwal ya gargadi Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

Gwamnan ya kuma kirayi sauraran jiga-jigai da masu fada a ji na kasar nan akan su tashi tsaye domin ceto wannan kasa daga tafarkin da ta nufata a halin yanzu na rugurgujewa.

A yayin kausasa harshen sa ga yanayin jagoranci a kasar nan, Tambuwal ya bayyana cewa ana bukatar shugabanni masu hangen nesa da zasu ribaci albarkatun kasar nan wajen ceto al'ummarta daga kangi na talauci.

KARANTA KUMA: Daukar Aiki: Ba za mu dauki wadanda ba su cika sharudda da Ka'aidojin mu ba - FRSC

Kazalika Tambuwal ya bayyana dalilin sa na sauya sheka zuwa PDP, inda ya ce mulkin kama karya gami da zalunci suka fatattaki duk wanda ya tsare daga jam'iyyar APC sakamakon dakile duk wata magudana ta kwararar romon dimokuradiyya a kasar nan.

Legit.ng kamar yadda gwamnan na Birnin Shehu ya bayyana ta ruwaito cewa, ya yanke shawarar tsayawa takara kujerar shugaban musamman domin kawo sauyi managarci wajen fidda kasar nan zuwa tudun tsira.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel