Karshen tika tika tik: Gwamna Kashim Shettima ya fatattaki kwamishinoninsa

Karshen tika tika tik: Gwamna Kashim Shettima ya fatattaki kwamishinoninsa

Gwamnan jahar Katsina, Kashim Shettima ya fatattaki dukkanin kwamishinoninsa daga aiki ba tare da wata kwakkwaran dalili ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarun Najeriya NAN ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya sanar da rusa majalisar zartarwar jahar Borno ne a ranar Talata, 25 ga watan Satumba ta bakin babban hadiminsa sakataren gwamnatin jahar, Alhaji Usman Jidda-Shuwa.

KU KARANTA: Wani mai neman samun aiki a hukumar karre haddura ta kasa ta fadi ya mutu a yayin atisaye

Gwamnan ya umarci dukkanin kwamishinonin jahar da su mika ragamar tafiyar da ma’aikatun da suke shuwagabanta ga manyan sakatarorin ma’aikatun kafin ranar Juma’a 28 ga watan Satumba.

Haka zalika Sakataren gwamnati Alhaji Usman ya bayyana musu sakon godiya tare da jinjina daga Gwamna Kashim duba da yadda suka sadaukar da rayukansu wajen samar da cigaba a ayyukan gwamnatin jahar Borno.

Daga karshe gwamnan ya yi ma kwamishinonin fatan Allah Ya basu nasara a dukkanin al’amuran da suka sanya a gaba, haka zalika ya mika sakon godiyarsa ga dukkanin jama’an da suka tallafa ma kwamishinonin wajen gudanar da ayyukasu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel