Kotu ta gayyaci Sanatan Najeriya a kan amfani da cheque din banki na bogi

Kotu ta gayyaci Sanatan Najeriya a kan amfani da cheque din banki na bogi

- Kotu ta aike wa Sanata Hope Uzodinma mai wakiltan Imo ta Yamma sammaci

- Ana zargin Sanatan ne da bayar da Cheque din bogi na N200 miliyan ga wasu kamfanoni

- Masu shigar da karar sunyi ikirarin cewa Sanatan ya dade ya na gujewa amsa gayyatar kotun

A yau, Talata ne wata kotun da ke zamanta a Kubwa, Abuja ta mika sakon gayyata da wani Sanatan Najeriya daga jihar Imo, Hope Uzodinma da ake zargi da bayar da cheque in bogi na N200 miliyan.

Sanatan dai yana wakiltan wasu kamfanoni biyu ne masu suna Smiec Engineering and Chemical Construction Company da Niger Global Engineering and Technical Company.

Kotu ta gayyaci Sanatan Najeriya a kan amfani da cheque din banki na bogi

Kotu ta gayyaci Sanatan Najeriya a kan amfani da cheque din banki na bogi
Source: Twitter

Alkalin kotun, Abdulwahab Mohammed ya wallafa samacin ne bayan lauyan masu shigar da kara, Oluwatosin Ojaomo ya bukaci kotun da gayyaci wadanda ake zargin saboda a cewarsa wadanda akayi karar ba su son amsa gayyatar kotun.

DUBA WANNAN: Rigima: Karuwar da wani direba ya dauko ta gudu da motar maigidansa ta N5m

Ojaomo ya shaidawa kotu cewa an bayar da umurnin kama wadanda a kayi kara tun a ranar 18 ga watan Satumba amma sun sun cigaba da yin kunnen uwar shegu da gayyatar kotun.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa an bayar da umurnin kama Uzodinma amma ya shaidawa kotu cewa bai aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Kazalika, NAN ta ruwaito cewa Chitex Ventures Limited da Chima Akuzie sun shigar da kara a kot kan wadanda ake zargin saboda basu takardan karbar kudi na bogi ta bankin UBA.

Alkalin kotun ya daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Oktoba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel